Hamɓararren shugaban ƙasar Gabon, Ali Bongo ya shafe shekaru 14 ya na mulkin Gabon. Ya hau mulki tun cikin 2009, bayan rasuwar mahaifin sa Omar Bongo, wanda ya shafe shekaru 42 ya na mulkin Gabon.
Omar wanda aka haifa cikin 1935, ya hau mulkin Gabon tun ya na ɗan shekara 33, a cikin 1967, shekaru bakwai bayan samun ‘yancin ƙasar.
Gabon ta samu ‘yanci a 1960, shekara ɗaya da Najeriya.
Omar Bango da ɗan sa Ali Bongo Ondimba, sun shafe shekaru 56 kenan su na mulkin Gabon.
An tsige Ali Bongo na Gabon daga kan mulki ya na ɗan shekara 64 a duniya.
Gabon wadda ta shiga Ƙungiyar Ƙasashe Rainon Ingila cikin 2022, ta faɗa hannun sojojin mulki, waɗanda suka yi zargin cewa zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar Asabar, cike ya ke ga maguɗi.
‘Bongo Zai Ci Gaba Da Rayuwar Sa Cikin ‘Yanci’: Jagoran Juyin Mulkin Gabon:
Jagoran juyin mulkin Gabon, Brice Oligui Nguema, ya ce hamɓararren shugaban ƙasa Ali Bongo zai ci gaba da rayuwa a cikin ‘yanci.
Zuwa lokacin da ake rubuta wannan labari dai sojojin juyin mulkin ba su kai ga naɗa shugaban ƙasa ba tukuna, kuma Nguema ya ce shi ba ya ƙwaɗayin dole sai ya yi mulki.
An ruwaito Ali Bango ya riƙa buga wayoyi a ƙasashe daban-daban, ya na so “su ce wani abu mana.”
Idan ba a manta ba, an yi kukan tafka maguɗi a zaɓen 2016, haka a 2019 sojoji sun yi yunƙurin juyin mulki, saboda zargin yin maguɗi a zaɓen da aka ce Ali Bongo ɗin ne dai ya ƙara yin nasara.
Allah ya albarkaci Gabon da ma’adinan ‘manganese’, wanda da shi ake yin ƙarafa da batira. Kuma ta fi kowace ƙasa samar da wannan ma’adinai a duniya.
Akwai kamfanin Eramet na ƙasar Faransa mai aikin haƙar ma’adinan, wanda ya ɗauki masu aikin haƙo ma’adinai yar su 8000 a Gabon.
Yanzu haka aikin haƙar ma’adinan ya tsaya cak, tun bayan kifar da gwamnatin Bongo da jijjifin safiyar Asabar ɗin nan.
Sojojin Mulkin Gabon dai sun ce Ali Bongo na tsare a gidan sa.
Discussion about this post