Kwanci tashi asarar mai rai, inji masu iya magana, a yau Jihar Jigawa ta ki shekaru 32 da kirkira. Jihar da a ka yi ta domin raya karkara. A yanzu za a iya cewa san barka.
A shekarun nan na Jigawa 32, koba komai an samu gagarumin cigaba a fannoni daban daban, kama daga harkar ilimi, harkar lafiya dan bunkasa karkara, kusan a yanzu Jihar Jigawa na da ga cikin jihohi masu isassun hanyoyin mota da suka hade muhimman garuruwa a jihar.
A yanzu jihar nada issasun makarantu da asibitoci, sannan na kan gaba wajen samar wa al’umar su.
Sai dai kash, a wannan karnin, babban kaluballen da ke addabar jihar shine karuwar talauci a tsakanin al’uma.
Daga cikin abin da ke kara wannan talauci shine rashin aikin yi, mussaman tsakanin matasa.
Yawan mutanen Jigawa ya karu da sama da kashi hudu koma biyar, a yanzu a na maganar, al’ummar Jigawa sun kai kusan mutane miliyan bakwai.
Yawan karuwar mutane ya hana tattalin arzikin wannan jiha, wannan ya haifar da karuwar rashin aikin yi a tsakanin matasa.
Kusan za a ce dukkanin aiyukan da su ka shafi karatun boko, kusan kashi saba’in gwamnatoci ne suke samar da shi, saboda karancin manyan kamfanoni ko masana’antu da su iya bawa matasan nan aikin yi.
Yanyin da gwamnatocin bata suka samu kansu da kuma yadda suka tafiyar da aiyukan su, wannan ya janyo rashin daukan aiki a guraben gwamnati wadatacce da zai bawa matasan nan abin yi.
Koda tsare-tsare na bayar da tallafi da samar da jari ga wannan matasa, shima ya kasa yin inganci da zai ceto wannan matasa.
Rashin aikin yibga matasa ba karamin tasgaro ya ke kawo ba wajen bunkasa tattalin arziki dama samar da tsaro.
Shin a wannan lokaci da saban gwamna Malam Umar Namadi ke jagoranta, kan iya kawo karshen wannan matsalar?
Ganin yadda gwamnatin a farkon hawanta ta kafa sabuwar hukuma da zata kula da harkar matasa da samar da aiyuka, ko zata yi tasiri wajen samawa wannan matasa aiyuka yi.
Amma mu tuna a baya ma fa, gwamnatin da gabata tayi kamanceceniyar wannan aikin, amma har yanzu matsalar aikin yi a tsakinin matasa ba karamin kalubale bane.
alhajilallah@gmail.com
Discussion about this post