Kamfanin NNPCL ya ƙaryata ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa cewa za a ƙara kuɗin fetur daga N617 zuwa N720 zuwa N750 kowace lita.
Haka NNPCL ya bayyana a cikin sanarwar da ya yi a shafin sa Tiwita, ranar Litinin da dare.
Ya ce maganar duk ji-ta-ji-ta ce da ƙadda-ƙanzon-kurege maras tushe balle makama.
“Ya ku kwastomomi masu sayen fetur, mu na gaishe. Kuma mu na yabawa da yadda ku ke ci gaba da shan fetur. To muna sanar da ku cewa ba mu da niyyar ƙara kuɗin litar fetur kamar yadda ake ya yayatawa.
“Muna roƙon ku da ku ci gaba da sayen litar fetur a farashin sa na Naira 617 a faɗin ƙasar nan, a sauƙaƙe.” Inji sanarwar NNPCL.
Fetur dai ya fara gudun famfalaƙin tsere wa talaka daga ranar da Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin fetur, tun a wurin rantsar da shi, kafin ma ya kai ga shiga ofis.
Sai dai kuma bayan an yi ƙarin lita zuwa N617, sai Shugaban NNPC, Mele Kyari ya ce ba ruwan Gwamnati da ƙarin kuɗin fetur, sharrin kasuwa ce, wata rana za ta karya farashin warwas.
Shugaban NNPCL, Mele Kyari, ya bayyana cewa babu ruwan Gwamnatin Tarayya da ƙarin kuɗin fetur.
Kyari ya bayyana haka ga manema labarai, bayan ganawar sa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.
“Mutum za shi kai kaya a kasuwa, amma sayarwa ko sayowa da sai yadda kasuwa ta yanke.
“Saboda haka akwai wadataccen fetur da za ya yi kwana 32 a wadace.
“Wata rana kuma farashin ƙasa zai yi warwas. Ya dogara ne da yadda kasuwa ke sharafi da kuma lokacin da ta ke tashi da hauhawar farashi.” Cewar Mele Kyari.
Shi kuma Shugaban
NMDPRA, Farooq Ahmed, ya ce wasu dalilan tashin farashin fetur, har da hauhawar farashin ɗanyen mai a duniya.
‘Yan Najeriya zuwa yanzu dai na a cikin damuwa, har Ƙungiyar ‘Yan jarida ta ƙasa, ta bayyana cewa ƙarin kuɗin fetur zuwa 617, ba shi da bambanci da dukan-kabarin-kishiya.
Sakataren Ƙungiya na Ƙasa, Sha’aibu Liman ya bayyana haka a ranar Talata, tare da bada shawarar a gaggauta cire kari da aka yi ba da bata lokaci ba.
Ta ce karin ya yi sanadiyar
tashin kuɗin motocin haya da farashin kayan abinci.
Litar fetur ta koma N617 a
gidajen man NNPC, wato farashin gwamnati.
An shiga gagarumar tsadar fetur, har ta kai farashin litar fetur ɗaya a gidan mai na NNPCL.
Haka ya tabbata a FCT Abuja da kewaye, a ranar Talata.
Wakilin mu ya ga ana sayar da lita ɗaya 617 a Wuse da kewaye. Lamarin ya faru wata ɗaya bayan da aka cire tallafin fetur, har lita ɗaya ta kai 537.
A wasu yankunan cikin jihohi lita ɗaya ta tafi har 568. Mai magana
da yawun NNPCL, Garbadeen Mohammed, ya ce a ba shi lokaci, zai yi bayani.
Wannan kari ya zo lokacin da yawan fetur ɗin da ake saye a kullum a Najeriya ya ragu da kashi 35 bisa 100.
Shugaban MDPPRA, Ahmed Farook, ya ce a yanzu fetur ɗin da ake saye a kullum lita Milyan 46.38 ne. Kafin cire tallafin fetur kuwa, a kan sayar da lita miliyan 65 ce a kullum.
Ya ce daga cikin waɗanda aka ba lasisin shigo da fetur, kamfanoni 3 ne kaɗai su ka shigo da fetur.
Tsadar fetur ta sake matsa lamba a lokacin da gwamnatin Bola Tinubu ke shirin bayar da tallafin kuɗaɗe domin rage wa marasa galihu raɗaɗin tsadar rayuwa.
A cikin ƙasa da dama sun koma shiga motocin haya saboda tsadar fetur.
Wasu kuma cewa su ke yi wannan tsadar rayuwa za ta iya yin tasirin da matasa za su ƙara shiga ruɗanin tafka laifuka a cikin al’umma.
Discussion about this post