An gargaɗi Gwamnatin Najeriya cewa kasar nan da Afrika ta Yamma za su afka cikin gagarimar matsala da fantsamar rikice-rikicen, matsawar aka yi kuskuren afka wa Jamhuriyar Nijar da yaƙi.
Ofishin Tsinkayen Sakamakon Zartas da Matakan Gwamnati Bisa Kuskure (OSPRE) ne bayyana waɗansu matsaloli 15 da ya ce Najeriya da ma Afrika ta Yamma za a fuskanta, inda ofishin ya nuna cewa babu alheri kwata-kwata a shirin kai wa Nijar hari don a dawo da dimokraɗiyya da ƙarfin tsiya a ƙasar.
OSPRE dai ofishin gwamnatin tarayya ne mai tsinkaye, hasashe da hango wasu matsalolin da za iya fuskanta nan gaba, tare da fitar da gargaɗi idan aka zartas da hukuncin da mafita ba ce, a kan wata matsala.
Ofishin OSPRE ya ce yin amfani da ƙarfin soja a matsalar Nijar ko kaɗan ba mafita ba ce, sai ma sake afkawa cikin wata sabuwar fitinar da za a yi.
Gargaɗi Da Shawarwarin Ofishin OSPRE Ga Najeriya Da ECOWAS:
1. ECOWAS sun janye tunani da shirin afka wa Nijar da yaƙi. Saboda hakan zai jefa Nijar cikin gagarimar matsalar tsaron da za ta addabi Afrika ta Yamma baki ɗaya.
2. Najeriya da ECOWAS su yi duk yadda za su yi, su haramta wasu wasu manyan ƙasashen waje yin amfani da ƙarfin soja, domin duk masifar da za ta samu Nijar, su ma sai ta shafe su.
3. Magance matsalar Nijar cikin lumana mafi alheri ga zaman lafiyar Najeriya, bisa la’akari da matsalar tsaron da ake fama da ita.
4. Tilas Shugaban Najeriya, kuma Shugaban ECOWAS, Bola Tinubu ya yi da muhimman batutuwa guda uku, kafin tunanin afka wa Nijar da yaƙi.
5. Afka wa Nijar da yaƙi zai harzuƙa ƙasar ta janye sojojin ta daga Gamayyar Rundunonin Haɗin Guiwar Yaƙi da Ta’addanci (MNJTF).
“Saboda idan Nijar ta janye daga MNJTF, to duk wata nasarar da aka samu wajen daƙile Boko Haram daga kan iyakokin ta, za ta zama koma-baya, za a koma gidan-jiya.”
6. Zaman lafiyar Nijar zaman lafiyar ‘yan Najeriya ne masu zaman gudun hijira a Nijar.
8. Zaman lafiyar Nijar gagarimin sassauci ne ga Najeriya, domin tsaro a Nijar ya na sauƙaƙa fantsamar matsalolin Libiya zuwa cikin Najeriya.
9. Yin amfani da ƙarfin soja a Nijar, zai ruguza zaman lafiya da ci gaba a yankin Sahel baki ɗaya.
10. Yawancin sojojin da ECOWAS za ta tura Nijar, duk ‘yan Najeriya ne. Saboda haka za a sake tattago wa sojojin Najeriya wani sabon jidali, alhali ga jidalin cikin gida da su ke fama da shi, inda yanzu haka aka tura sojoji jihohi 32 na Najeriya su na gaganiyar aikin tsaron ƙasa a Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas da Kudu maso Gabas.
11. Azarɓaɓin yin amfani da sojoji a matsalar da ba ta kai ga hakan ba, za ta buɗe wa gungu-gungun ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda wasu ƙoƙofin kai hare-hare da mamayar yankuna a sauƙaƙe.
12. Gaggawar Tinubu ta son afka wa Nijar da yaƙi, zai bayar da ƙofar yi masa kallon ɗan bangar ƙasar Faransa. Hakan kuwa zai ƙara ruruta wutar kallon-hadarin-kajin da ke tsakanin ƙasashen ECOWAS Rainon Ingila da ƙasashen ECOWAS Rainon Faransa.
13. Ganin yadda a yanzu ake ƙara nuna tsabar Faransa a ƙasashen da ta yi wa mulkin mallaka, za a fassara afkawar sojojin Najeriya da na ECOWAS cikin Nijar a matsayin sojojin mamaya, ba sojojin ceto ƙasar ba.
14. Yaƙi da Nijar zai ruguza haɗin kan ECOWAS, domin tun a yanzu alamomin rugujewar sun fito, yayin da Mali, Gini da Burkina Faso su ka fito ƙarara su ka goyi bayan sojojin juyin mulkin Nijar. Har ma su ka ƙaurace, tare da ƙin turo Manyan Hafsoshin Tsaron ƙasashen su a taron Manyan Hafsoshin Tsaron Ƙasashen ECOWAS.
Shawara Ga Najeriya Da ECOWAS Dangane Da Nijar – OSPRE:
15. Abu na farko shi ne ku tattauna da sojojin mulkin Nijar, su saki Mohammed Bazoum, shi da iyalin sa a ba shi mafakar siyasa a ɗaya daga cikin ƙasashen ECOWAS.
16. A tattauna da sojojin mulkin Nijar su shata tantebur ɗin gaggauta maida Nijar a turbar dimokraɗiyya.
17. A gaggauta tsara yadda za a kwaso ‘yan Najeriya daga Nijar ko daga wata ƙasar da Faransa ta yi wa mulkin mallaka, matsawar dai su na fuskantar wata bazarana yanzu haka a can.
Discussion about this post