Shugaban mulkin soja na Nijar Abdoulrahmone Tchiani ya ce har yanzu kofofin su na yin sulhu a buɗe su ke, amma kuma idan ECOWAS ta ce za ta far wa kasar, lallai za ta fuskanci fushin Sojojin Nijar.
Bayan haka BBC Hausa ta ruwaito cewa
Daruruwan matasa sun taru a birnin Yamai domin ɗaukarsu aikin sa-kai a Nijar, a wani yunƙuri na kare ƙasar daga farmakin Ecowas.
BBC ta buga cewa Rahotonni sun nuna cewa an shirya ɗaukar matasan aikin ne domin mayar da martani idan ƙungiyar Ecowas ta kai wa ƙasar farmaki.
Ana gudanar da aikin ne a wani ɓoyayyen wuri a Yamai babban birnin ƙasar, to sai dai an hana ‘yan jarida zuwa inda ake aikin ɗaukar ‘yan sa kan.
Ba a dai sani ba ko sojojin da suka yi juyin mulkin na sane da aikin ɗaukar ‘yan sa-kan.
Rahotonni da ke fitowa daga ƙasar sun ce, ana sa ran ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar-baya a ƙasar za su tallafa wa sojojin da magunguna da kayan aiki sauran dabaru idan Ecowas ta ƙaddamar da yaƙi a ƙasar.
A ƙarshen taron hafsoshin tsaron ƙasashen Ecowas da aka gudanar da Ghana ne aka amince da saka ranar far wa Nijar da yaƙi.
To sai dai ƙungiyar ba ta bayyana takammiyar rana ba, amma ta ce dakarunta a shirye suke domin fara kai farmaki.
Discussion about this post