Hukumar NDLEA ta bayyana cewa daga Janairu zuwa Agusta ta kama haramtattun kwayoyi suka kai naira miliyan 56.9 da nauyinsu ya kai kg 3,091.032 a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Shugaban hukumar Kabir Tsakuwa ya sanar da haka ranar Laraba da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a Abuja.
Tsakuwa ya ce haramtattun kwayoyin da hukumar ta kama sun hada da ganyen wiwi, hodar ibilis, Methamphetamine, tramadol, rohypnol, Diazepam, ecstasy da megadon.
Ya ce a tsakanin wannan lokaci hukumar ta kama masu safarar muggan kwayoyi mutum 343 da a cikinsu akwai maza 328 da mata 15.
Tsakuwa daga cikin yawan mutanen da suka kama hukumar ta kai mutum 188 kotu da a cikinsu kotu ta yanke wa mutum 126 hukunci.
Tsakuwa ya ce daga Janairu zuwa yanzu hukumar na kula da mutum 33 dake fama da matsalolin tabuwar hankali sannan hukumar ta sallami mutum 102 da ta tabbatar sun warke daga irin wannan matsaloli.
Ya ce hukumar za ta hada hannu da sauran jami’an tsaro domin kama masu sha da safarar muggan kwayoyi a Abuja.
Discussion about this post