Shugaba Bola Tinubu ya cire Babban Daraktan Hukumar Katin Ɗan Ƙasa (NIMC), Aliyu Aziz, ya maye gurbin sa da Injiniya Bisoye Coker-Odusote a matsayin Shugaban Riƙo.
An cire Aliyu Aziz, wanda Tinubu ya umarci ya tafi hutu, kwanaki 90 kafin lokacin ritayar sa.
Kakakin Yaɗa Labaran Tinubu, Ajuri Ngelale, bai bayyana dalilin cire Aliyu Aziz tun watanni uku kafin lokacin yin ritayar sa ba. Amma dai ya ce, sauke shi zai ba shi damar tafiya gida ya yi shirye-shiryen yin ritayar sa nan da 24 Ga Nuwamba.
Sallamar ta sa za ta fara ne daga ranar 24 Ga Agusta, 2023, inda shi kuma Bisoye zai ci gaba da zama shugaban riƙo, har sai ranar 24 Ga Nuwamba, 2023 sannan zai zama cikakken Babban Daraktan NIMC, kuma shugaban hukumar.
Haka kuma Tinubu ya naɗa Yusuf Baba a matsayin Daraktan Ayyukan DTAC.
Nadin Yusuf ya biyo bayan cikar wa’adin aikin tsohon Daraktan DTAC, Pius Osunyikanmi.
“An yi wannan naɗin nan take, kuma zai fara aiki nan take.” Haka Kakakin Yaɗa Labaran Tinubu, Ajuri Ngelale ya bayyana a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Talata.
Tuni dai Shugaba Bola Tinubu ya ci gaba da naɗe-naɗe a gwamnatin sa, inda a ranar Litinin ya rantsar da sabbin Ministoci 45 da ya naɗa.
Cikin waɗanda aka naɗa ɗin akwai Mohammed Idris, wanda a yanzu shi ne Ministan Yaɗa Labarai, Abubakar Badaru, tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, a yanzu shi ne Ministan Tsaro, sai kuma tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, wanda a yanzu shi ne Ƙaramin Ministan Tsaro.
Discussion about this post