Yanzu dai ko ina ka shiga za ka ji ana hirar cewa mazan aure sun yi matukar wuyan samu. Ga dai ‘yan matan a gari amma ko a samu wanda zai fito ya bigi kirji ya ce ya ji ya gani da ke za ayi shine abin fa da kamr wuya.
Sai dai kuma duk da haka wakiliyar mu ta bincika mana wasu dabi’u da hanyoyi da mace za ta bi domin samin mijin arziki a coci ba tare da sha wahala ba ko kuma an yi ta kai ruwa rana.
Coci na daga cikin wuraren da ake gamayya sosai tsakanin mata da maza domin bauta da yin ibada.
Hakan ya sa idan mai rabo ya dace sai wata ko wani yayi wuf da shi sai gidan aure.
Hanyoyin da za ka bi kuwa shine
1 – A rika halartar tarukan kungiyoyin matasa a Coci: A irin wuaren tarukan ne aka fadakar da matasa sanain muhimmancin yin rayuwa mai amfani, tsare gaskiya da sanin ya kamata. Sannan kuma da dagewa akan gaskiya a koda yaushe. Irin wadanna wurare, za ka iya ko ki ya dacewa da saurayi ko budurwa mai hankali da tarbiya domin a yi aure.
2 – Haka kuma idan mutum ya fadi wani abu da ya same shi mai daukan hankali, wanda zai saka mutane cikin tunai mai zurfi a Coci, kama ko dai tausayi ko kuma ace abu ne mai ban mamaki ko al’ajabi ko kuma cigaba.
3 – Yawaita yin aikin sa kai don samun lada a coci
Yin aikin lada kamar koyarwa, yi wa mutani dawainiya a coci duk sun saka a kulla soyayya tsakanin mutane har ya kai ga an yi aure.
4 – Shiga kungiyoyi a coci
Akwai kungiyoyi biyu daga cikin kungiyoyin da suke coci da masu neman saamari ko matan da za su aura. Wadannan kungiyoyi sun hada da kungiyoyin matasa da mawaka.
5 – Kwaliya: Mace ‘yar kwalisa mai rangada kwalliya a koda yaushe ita ma za ta iya daukar hankalin maza su yi sha’awarta su neme ta da aure.
Discussion about this post