Ministar Al’adu Hannatu Musawa ta ƙaryata rahoton da wasu kafafen yaɗa labarai suka watsa wai ta ce ‘ Bata karya doka ba ta na minista kuma ta na aikin yi wa kasa hidima, wato NYSC.
A takarda da mataimakin Darektan yaɗa labarai na ma’aikatar Al’adu, Suleiman Haruna ya fitar ranar Lahadi, bisa umarnin minista Musawa, ya ce minista ba ta fidda wata takarda da ake kafa hujja dashi a kafafen yaɗa labarai wai ta fito daga wurinta ne.
” Minista Musawa ba ta fidda wata takarda ba cewa wai ta ce ‘ ba ta ga laifin da ta aikata ba don ta na minista kuma ta na aikin hidima wa kasa, NYSC.’
” Babu gaskiya a cikin wannan batu, dalilin haka minista Musawa ta ke kira ga ƴan jarida su riƙa tantance abubuwan da suke sakawa don gudun watsa abinda ba haka ba.
Tsakanin Musawa da Hukumar NYSC
Ana ci gaba da samun karin bayanai game da cecekuce da kai ruwa rana da ake yi tsakanin minitan Al’Adu, Hannatu Musawa da Hukumar kula da masu yi wa kasa hidima, wato NYSC da ya ki ci ya ki cinyewa.
Tun bayan rashin bayyana shaidar kammala horo na yi wa kasa hidima wato NYSC da Hannatu Musawa ba ta iya yi a gaban majalisar dattawa ba a lokacin da ake tantance ta, abin ya fito bainar jama’a da mutane ke ta tofa albarkacin bakin su game da batun.
PREMIUM TIMES ta bi diddigin maganar kuma ta gano cewa akwai maganganu masu dama akai wanda ke nemen sai an yi wa mutane dalla-dalla domin su gane me ke a ciki game da shaidar kammala horo na yi wa kasa hidima wanda ya tsaya wa Hannatu a wuya, ya zame mata kashin kifi.
PREMIUM TIMES ta gano cewa tun farko dai bayan kammala karatun ta na digiri a jami’ar Landan, Hannatu ta dawo Najeriya domin yi wa kasa hidima. Hukumar NYSC ta tura jihar Ebonyi domin yin aikinta a can kuma an tura ta ma’aikatar shari’a ce ta jihar.
Sai da kuma bayan ta yi wata biyar a can sai da nemi a dawo da ita Kaduna. Tun da aka maido ta Kaduna, bincike daga takardun hukumar sun nuna bata karisa aikin yi wa kasa hidima ba, dalilin da ya sa aka ki bata shaidar Kammala aikin yi wa kasa hidima na NYSC.
Sai dai kuma duk da wannan korafi da zargi da NYSC ta yi akan Musawa, a wasu lukutta a baya ta bayyana cewa ta kammala aikin yi wa kasa hidima har an bata shaidar kammala NYSC. Musawa ta ce shaidar kammalawar ya kone a gobara da ta yi a gidan ta na Abuja a shekarar 2019.
Har ta kai ga samun shaidar rahoton ‘yan sanda akai cewa Satifiket din kammala NYSC dinta ya kone a gobara.
Amma kuma daga baya, bayan NYSC ta ki amincewa da wannan batu na ta, bincike sai ya nuna cewa lallai Musawa bata karbi shaidar kammala NYSC ba, ta shirga karya ne cewa da ta yi wai ta amsa, amma ya kone a gobarar gidanta, NYSC ta ce bata kammala hidimar ba ballatana a bata shaidar kammalawa.
Bayan haka PREMIUM TIMES ta gano cewa Musawa ta rika rubuta wasika har ga ministan matasa, Sunday Dare a lokacin gwamnati Muhammadu Buhari domin ya shiga tsakani. Sai dai hakarta bai cimma ruwa ba domin shima dai bai iya gane hawa ba ballanta na sauka game da maganar. Binciken da ya yi shime ya gano cewa tabbas, hukumar NYSC ce za ta iya warware wannan matsala. Kuma ta ce a bisa duka bayannan ta Musawa ba ta kammala aikin bautar kasa ba.
A shekarar 2020, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabe ta a matsayin kwamishina ta kasa mai wakiltar shiyyar arewa maso yammacin Najeriya a hukumar fansho ta kasa (PENCOM).
Sai dai dalilin rashin bayyana shaidar kammala NYSC ya sa ba ta iya aikin ba. Haka dole ta hakura.
Inda ake yanzu
Direktan yada labarai na hukumar NYSC, Eddy Megwa ya shaida cewa, tuni ai sake fidda sunan Musawa cikin masu bautar kasa na wannan shekara kuma ta nan ta karisa watannin ta 8 da kauce musu a baya yanzu haka a Abuja.
An haifi Musawa a ranar 1 ga Nuwamba 1974, sannan Musawa ta kammala karatun digiri a Jami’ar Buckingham da Makarantar Shari’a ta Najeriya kafin ta cika shekaru 30 don haka ta cancanci yin hidimar kasa.
Dokar NYSC ta ce dole duk dan kasa kuma dalibi a Najeriya, ya yi aikin yi wa kasa hidima, idan ya kammala karatun Digiri ko HND, kafin ya shekara 30 da haihuwa.
Discussion about this post