Gwamnantin Tarayya ta sake garzayawa kotu a ranar Talata, ta na neman ta janye tuhumar mallakar bindigar da ta ke wa tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Ta bayyana aniyar neman tuhumar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas.
Daraktan Gurfanar da Waɗanda Ake Zargi na Gwamnatin Tarayya, a Ma’aikatar Shari’a, Abubakar Mohammed ne ya sanar wa kotun haka, a ranar Talata, yayin da ya ke magana da baki, ba a rubuce ba a gaban kotun.
Ya shaida wa Mai Shari’a Nicholas Oweibo hakan bisa dalilin wasu ƙarin abubuwan da Gwamnatin Tarayya ta binciko kan Emefiele.
Bayan fitowa daga kotu, Mohammed ya shaida wa manema labarai cewa, “Gwamnatin Tarayya ka iya dawowa kotu da ƙarin canje-canje a kan Emefiele.”
Zargin Mallakar Bindigar Da Gwamnatin Tarayya Ta Janye Kan Emefiele:
Zargin Mallakar Bindiga: Kotu ta bada belin Emefiele, ta ce bai aikata laifukan da za a ci gaba da tsare shi ba.
Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta bada belin tsohon Shugaban Babban Bankin Najeriya,
CBN, Godwin Emefiele.
SSS sun gurfanar da shi a ranar Talata, shi ne
lauyan sa ya ce a ba shi beli.
Mai Shari’a ya ce za a iya belin Emefiele a kuɗi ₦20,000,000.00.
SSS sun gurfanar da Emefiele kotu, a madadin Gwamnatin Tarayya, ta gurfanar da tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Emefiele a kotu.
SSS sun maka shi Babbar Kotun Tarayya, inda ake zargin sa da mallakar
bindiga da harsashe.
An gurfanar da shi a ranar Alhamis, amma ba a sa ranar da za a fara shari’ar ba.
Ana tsare da shi tun a ranar 10 Ga watan da ya gabata, har kotu ta yi gargadi a sallame shi Ko a gurfanar da shi.
Sai dai kuma maimakon a ga zargi da ake yi masa da ta’addanci da farko, ya ana tuhumar sa da mallakar hargitsa bindiga da harsashi.
Babbar Kotun Tarayya ta ce wa SSS ‘Ku gurfanar da Emefiele a kotu, ko ku sake shi.’
Babbar Kotun Tarayya ta gargaɗi SSS cewa su gaggauta sallamar tsohon Gwamnan ta saɓa doka ce ƙarara.
Lauyoyin sa su ka garzaya kotu domin su yi bayani cewa SSS sun toshe hanyoyin ganawa da Emefiele ɗin.
Bayan kama shi, wasu ‘yan raji su ka ce EFCC da ICPC ke da alhakin su kama Emefiele, amma ba aikin SSS ba ne.
Cikin su har da tsohon Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA), ya bayyana abin da ya kira “damuwar sa”, dangane da kamun da Hukumar Tsaro ta SSS ta yi wa dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Agbakoba ya ce babu wani ƙorafi don an dakatar da Emefiele, amma dai shi bai ga dalilin da zai sa SSS su kama shi ba, tunda su dai babu ruwan su da shiga lamarin laifukan da su ka shafi harkokin tattalin arziki ko kuɗaɗe.
“Aikin SSS shi ne tabbatar da tsaron cikin gida, wato cikin ƙasa. To me zai kai su ga kama Emefiele?
“Abin mamakin shi ne yadda sauran hukumomin da ke da haƙƙin binciken harkokin zambar kuɗaɗe su ka yi shiru, har yau ba su ce komai ba dangane da Emefiele, tun bayan dakatar da shi. Sai kawai ji mu ka yi SSS sun ce ya na hannun su. In dai ba zargin aikata zagon ƙasa ga gwamnati ba, me zai kai SSS su kama shi?” Inji Agbakoba.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin kama Emefiele da SSS yi, sannan aka jefa shi magarƙama bayan Tinubu ya dakatar shi.
A cikin labarin kuma an bayyana yadda SSS su ka zarge shi da laifin taimaka wa ‘yan ta’adda da kuɗaɗe, amma kotu ta hana kama shi a cikin Disamba, saboda rashin ƙwaƙƙwarar hujja.
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (SSS) ta bayyana cewa ta kama dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele.
DSS sun kama shi, ba da daɗewa ba bayan Gwamnatin Tarayya ta bayar da sanarwar dakatar da shi.
Sanarwar da damƙe Emefiele ta fito daga bakin Kakakin Yaɗa Labaran SSS, Peter Afunanya, a cikin wata sanarwar manema labarai da ya raba, ya aiko wa PREMIUM TIMES.
Idan ba a manta ba, cikin watan Disamba, 2022 SSS sun nemi kama shi domin zargin ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda, amma kotu ta hana su, saboda rashin ƙwaƙƙwarar shaida.
Discussion about this post