Gwamnatin tarayya ta ce ta ware qa kowacce jiha a kasar nan, har da Abuja, naira biliyan 5 a waiwayi talakawa su ɗan ji sanyi-sanyin raɗaɗin cire tallafin mai.
Bayan haka kuma an naɗa kwamiti domin ganawa da kungiyoyin Kwadago domin a tattauna da su.
Wannan wasu ne daga cikin shawarwarin da aka cimma a taron majalisar tattalin arzikin kasa karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a fadar gwamnati da ke Abuja.
A Wata sanarwa da ofishin mataimakin shugaban kasar ya fitar bayan taron ta ce mambobin kwamitin sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara; Gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo; Shugaban kungiyar gwamnonin Progressives Forum, Hope Uzodinma na jihar Imo; Shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Bala Mohammed na jihar Bauchi, da gwamnan jihar Abia, Alex Otti.
Majalisar ta kuma samu rahotannin ci gaban da ake yi kan rabon shinkafa da hatsi da taki da sauran kayayyaki ga Jihohi da kuma tallafin kudi Naira biliyan 5 da gwamnatin tarayya ta bayar tare da yabawa babban bankin Najeriya CBN da hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA.
Discussion about this post