Gwamnatin jihar Katsina ta hana amfani da babura da Keke NAPEP na haya a kananan hukumomi 19 a jihar.
Kwamishinan tsaro na jihar Nasiru Mu’azu ya ce dokar zai fara aiki daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe.
Mu’azu ya ce gwamnati ta kafa wannan doka a kananan hukumomin da suka fi fama da rashin tsaro a jihar.
“Kananan hukumomin da wannan doka ya shafa sun hada da Sabuwan, Dandume, Funtua, Faskari, da Bakori.
“Saura sun hada da Kankara, Danja, Kafur, Malumfashi, Musawa, Matazu, Danmusa, Safana da Dutsinma.
“Sannan da Kurfi, Charanchi, Jibia, Batsari da Kankia.
“Gwamnati ta saka wannan doka ne domin Samar da tsaro da zaman lafiya a fadin jihar.
Discussion about this post