Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani ya rage kudin manyan makarantun jihar Kaduna wanda tsohon gwamna Nasir El-Rufai ya kara a zamanin mulkin sa.
Gwamna Sani da yake zantawa da manema labarai a afadar gwamnatin jihar, ya shaida cewa bayan dubawa da gwamnatin sa ta yi da kuma rage matsa da mutane ke ciki a halin yanzu ya ga ya dace gwamnati ta rage kudin makaranta domin iayaye su iya biya wa ya’yan su.
Idan ba a manta ba babu yadda ba a yi da tsohon gwamna El-Rufai ya hakura da wannan kari amma ya kafe, ba a isa ba dole sai an laft6a wa talaka wannan kudi kuma ya biya, abinda yayi sanadiyyar wasu da dama dole suka hakura da karatu a lokacin.
Uba ya ce daga yanzu daliban Jami’ar KASU za su rika biyan naira 105,000 ne mai makon naira 150,000 da aka saka musu a baya. An yi ragin kashi 30 cikin 100 na abinda aka biya a baya.
Kwalejin Kimiyya ta Nuhu Bamalli kuma, naira 50,000 ne za su rika biya maimakon naira 100,000.
Kwalejin Kiwon Lafiya na Shehu Idris – Za arika biyan naira 70,000 maimakon naira 100,000 da ake biya a babbar Difloma, HND.
Karamar Difloma kuma za a rika biyan naira 52,000.
Kwalejin koyon Aikin Ungozoma na kaduna da ake biyan naira 100,000, za a rika biyan naira 70,000 ne yanzu.
Gwamna Uba ya ce wannan rage kudi da gwamnati ta yi ya zama dole domin sauwake wa iyaye su iya biyan kudin makarantan yayan su.
” Bayan matsi da ake ciki na radaddin cire tallafin mai, wannan wata hanya ce da muka ga ya dace mu dauka domin rage wa iyaye matsin rashi da ake fama da shi. Sannan kuma da ganin ba a bar kowa a baya ba wajen samun ilimi.
Wasu iyaye da suka tattauna da PREMIUM TIMES HAUSA sun godewa gwamna Sani da yi masa fatan alkhairi a mulkin sa, bayan nuna farin cikin su ga wannan matsaya da gwamnati ta dauka.
” Ni dai ina da ‘ya’ya da suke karatu wa manyan makarantun Kaduna, dole in gode wa gwamna Uba Sani bisa wannan kokari da ya yi na rage kudin makaranta. Ko naira 10 ne aka cire wallahi ya kyauta mana ballanta ma kune ne masu yawa a ka rage.” Hajiya Halima.
” Ni kaina wannan rage kudi da aka yi ya faranta mini rai tsakani da Allah. Mu na gani ya’yan mu da yawa suka daina zuwa makaranta, sannan gwamnatin El-Rufai ta ce ta ji ta gani, amma da yake wannan gwamna ya na da hangen nesa da tausayi, ga shi ya rage mana kudin. Muna godiya matuka. ” Inji Istifanus Malam
Discussion about this post