Gwamnatin jihar Kaduna ta samar da ingantattun kayan aiki wa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 290 a fadin jihar.
Gwamnan jihar Uba Sani a taron raba kayan da aka yi ranar Laraba ya ce gwamnatinsa za ta bunkasa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko domin mutane su rika samun kula na kiwon lafiya na zamani.
Ya ce baya ga haka gwamnati za ta horas da ma’aikatan lafiya domin su samu kwarewar kula da marasa lafiya a cibiyoyin kiwon lafiya na jihar.
“A lokacin da aka kafa wannan gwamnati mun yi alkawarin farfado da fannin lafiyar jihar ta hanyar samar da kwararrun ma’aikata, zuba kayan aiki da wata cibiyoyin da magunguna domin marasa lafiya.
“Za mu ba da ƙarfi wajen kula da lafiyan mutane domin farfado da tattalin arziki. Za mu farfado da tattalin arzikin karkara ta hanyar bunkasa ababen more rayuwa a wuraren.
“Burin mu shine wadannan matakai da muka dauka zai taimaka wajen inganta aiyukkan jami’an lafiyar da za a horas
Ya yi kira ga mutane da jami’an lafiya da su sa Ido wajen ganin an yi amfani da wadannan kaya yadda ya kamata.
Discussion about this post