Ƙazamin yaƙi ya ɓarke tsakanin ɓangarorin ‘yan ta’adda biyu – Boko Haram da ISWAP, kusa da Marte a Jihar Barno, wanda ya yi sanadiyyar kashe junan su fiye da mutum 100.
Wata majiyar jami’an tsaro wadda ke da masaniyar artabun da ‘yan ta’addar su ka a tsakanin su, ta ce faɗan ya yi muni sosai a ranar Asabar, inda ɓangarorin biyu kowane ya yi asarar rayuka masu yawa.
PREMIUM TIMES ta ji daga majiya mai tushe cewa faɗan ya ɓarke tsakanin Boko Haram ‘yan ɓangaren Bakoura Buduma da kuma ISWAP a kan wanda ke da haƙƙin wani Yankin Tafkin Chadi.
An yi ta fafata yaƙin a yankin Bakuram a hayin Yankin Tafkin Chadi.
Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ISWAP ta yi ƙoƙarin yin ramuwar-gayya ce kan Boko Haram, ramuwar dakarun ta 60 da Boko Haram su ka kama, tare da wasu kwamandojin ISWAP ɗin su uku.
PREMIUM TIMES ta samu bayanin cewa wannan yaƙi shi ne mafi muni da ya faru a tsakanin ƙungiyoyin biyu, waɗanda a baya akwai jituwa a tsakanin su.
ISWAP dai a yankin ta na ƙarƙashin wani ne mai suna Abou Idris, tsohon Magayaƙin Boko Haram, wanda ya ɓalle ya koma cikin ISWAP.
“Kowane ɓangare ya yi asarar rayuka a yaƙin. Amma ISWAP sun fi kashe ‘yan Boko Haram da yawa.
“A yanzu da muke maganar nan da kai, su na can suna yi wa juna zabarin wuta kawai, har an kashe fiye da ‘yan ta’adda 100 daga kowane ɓangare.” Cewar wata majiyar mu.
PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Kakakin Hedikwatar Tsaron Sojoji ta Ƙasa, inda bai ɗaga kiran da aka yi masa ba.
Discussion about this post