Tsohon gwamnan Kaduna NAsir El-Rufai ya gargadi kungiyar ECOWAS da shugaban ta, shugaban Najeriya, Bola Tinubu da kada a kuskura a far wa jamhuriyar Nijar da yaki, yana mai cewa hakan zai kawo rashin zaman lafiya tsakanin mutanen yankin Arewacin Najeriya da kasar na Nijar.
El-Rufai wanda ya kusa zama ministan Tinubu amma abin ya faskara, ya yi wadannan rubuce rubuce ne a shafin sa ta X ranar Litinin.
El-Rufai ya ce far wa Nijar da yaki ba zai haifar da da mai ido ba, ya gargadin kungiyar ECOWAS da shugaban Kasa Tinubu da su janye wannan shawara.
” Mutanen Arewacin Najeriya da Nijar ‘yan uwan juna ne. Far wa Nijar da yaki kamar far wa Arewacin Najeriya da yaki ne. ku dai yi takatsantsan”
Tun bayan janyewa da yayi daga nada shi Minista El-Rufai ya fice daga Najeriya, ya koma makaranta a kasar Neitherland.
Amma kuma da dama daga cikin masu yin fashin baki a siyasar Najeriya sun bayyan cewa El-Rufai na fadin haka ne don ba shi cikin gwamnati.
” Ni dai a gani na da ace El-Rufai ya samu zama minista, ba zai fito ya fadi irin haka ba, ko da zai fadi zai yi shi cikin dabara ne. Domin Tinubu gaskiya ba Buhari bane, shi ya san abinda ya dace matuka kuma ya na yin nazari mai zurfi.
Discussion about this post