An gargaɗi ‘yan Najeriya su yi shirin guduwa daga mummunar ambaliyar da za ta faru nan ba da daɗewa ba, yayin da ƙasar Kamaru ta ɓallo ruwan Madatsar Ruwan Lagdo wadda ke yankin Garwa, Arewacin Kamaru.
Madatsar ruwan ta Lagdo ta na kan Kogin Benuwai ne.
Wata sanarwar da Salisu Umar, Daraktan Harkokin Afrika na Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ya fitar, ya ce an umarci Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), cewa ta gaggauta shirya gudanar da matakan gaggawar da za su taƙaita ɓarnar da ambaliyar za ta yi.
Haka kuma an umarci NEMA ta gaggauta sanar da jama’a irin ɓarnar da ambaliyar za ta yi idan Kamaru ta ɓallo ruwan dam ɗin na Lagdo.
“An umarce ni na sanar da cewa Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta samu wasiƙar gargaɗi daga Ofishin Jakadancin Kamaru da ke Najeriya cewa mahukuntan Kamaru sun shirya ɓalle ƙofofin madatsar ruwa ta Lagdo Dam, wanda ke kan Kogin Benuwai.
“Kamaru ta shirya ɓalle ruwan, saboda tsananin ruwan saman da ake yi ya cika dam ɗin har ya na tumbuɗi a Arewacin Kamaru.”
NEMA ta ce ta na aiki tare da ofishin ta da ke Jihar Neja, Benuwai da Kogi domin tabbatar da cewa an yi duk abubuwan da su ka wajaba don ganin ambaliyar ba ta yi mummunar ɓarna ba.
“Na gana da gwamnonin jihohin, inda na fayyace masu komai dalla-dalla. Bayan nan kuma na ƙara yin wani taron da su, na ƙara yi masu gargaɗi dangane da ambaliyar.
“Na bai wa gwamnonin shawarar cewa su gaggauta samar da ofisoshin gaggauta a ƙananan hukumomi, a kwashe cinkoson da ya toshe kwalbatoci da sauran su,” haka Mustapha Habeeb, Shugaban Hukumar NEMA ya shaida wa BBC Hausa.
Habeeb ya ce Kamaru za ta ɓallo ruwan, amma ba mai yawa ba, don kada ya yi mummunar ɓarna.
Idan ba a manta ba, ambaliya ta ci rayuka 612 a Najeriya, cikin 2022, kuma ta kori mutum miliyan 1 da 400,000 daga gidajen su.
Ambaliyar ta 2022 ta ruguza gidaje sama da 200,000, ta lalata gonaki masu yawan hekta 110,000.
Ministar Agaji, Jinƙai ta lokacin, Sadiya Umar ta ce an yi asara za ta kai ta Naira tiriliyan 4.2 sanadiyar ambaliya a 2022.
Kuma ambaliyar ta 2022, ta yi muni sosai sanadiyyar ɓallo ruwan Lagdo Dam da Kamaru ta yi a cikin Satumba, da kuma wasu dalilai.
Discussion about this post