Shugaba Bola Tinubu ya fito gabagaɗi domin share kukan al’ummar ƙasa musamman dangane da halin matsi da ake ciki.
A cikin wani tsakure da Kakakin Yaɗa Labarai Abdul’aziz Abdul’aziz ya wallafa, ya ce za a fito da yadda gwamnati ta shirya antayo maƙudan kuɗaɗe ta fannoni da dama domin ragewa mutane raɗaɗin gyaran karayar tallafin mai da ake ciki a halin yanzu. Ga kaɗan daga cikin tanade-tanaden:
1. Bawa masu masana’antu 75 jari mai rangwame har na naira biliyan ɗaya kowannen su. Wanda za su biya a tsahon watanni 60.
2. Masu matsaƙaita da ƙananan sana’o’i za su amfana da naira biliyan 125 domin haɓɓaka jarinsu.
3. Daga cikin waccan biliyan 125 gwamnati za ta bada jari kyauta (mai haɗe da sharaɗi) na naira 50,000 ga masu ƙananan sana’o’i mutum 1,300 a kowace ƙaramar hukuma.
4. Sauran biliyan 75 za su tafi wajen masu matsaƙaitan sana’o’i inda za a bawa mutum 100,000 rance mai rangwame na naira 500,000 zuwa miliyan ɗaya wanda za su biya a hankali cikin shakara uku.
5. Tunda sai da ruwan ciki ake janyo na rijiya, Shugaban Ƙasa ya bada umarnin fito da abinci har ton 200,000 tare da takin zamani ton 225,000 domin rabawa ga mabuƙata da manoma.
5. Nan ba da jimawa ba gwamnati za ta samar da ƙananan moticin bus masu amfani da gas har guda 3,000 domin kawo rangwame a kuɗin sufuri da jama’a ke fama da shi. Waɗannan motoci za a raba su ne ga kamfanonin sufuri domin gudanar da su.
6. Haka nan kuma gwamnati ta ware maƙudan kuɗaɗe domin noma hekta 500,000 a ɓanagarori daban-daban na ƙasar nan. Baya ga samar da abinci wannan shiri zai samarwa da matasa marasa aikin yi sana’a ta wucin-gadi.
7. Gaggauta aiwatar da tsarin gyaran albashin ma’aikata da zarar gwamnati ta cimma matsayi da ƙungiyoyin ƙwadago.
A ƙarshe, ga waɗanda suka saurari cikakaken jawabin za su ji yadda Shugaba Tinubu ya nuna tausayawa da halin da ake ciki, ya bada haƙuri, ya kuma sha alwashin ƙawo ƙarshen wannan yanayi cikin gaggawa da taimakon Allah.
Discussion about this post