An bayyana cewa an gano wata mahaɗar da ake karkatar da ɗanyen man fetur a Jihar Abiya, inda a duk wata Najeriya ke yin asarar ɗanyen mai na aƙalla Dala Miliyan 7.2.
Wata tawagar yin nazarin yadda ake satar ɗanyen mai ce wadda Shugaba Bola Tinubu ya kafa a Yankin Neja Delta ya ta gano wannan bututun da ake karkatar da ɗanyen man a ranar Asabar.
Haramtaccen wurin da ake karkatar da ɗanyen man dai ya na a Owaza ne a cikin Jihar Abiya. NNPCL ta ce ta bayyana haka a ranar Asabar.
Ta ƙara da cewa tawagar ta kuma ga irin mummunar ɓarnar da ake wa tattalin arzikin ƙasa ta hanyar satar fetur, manyan ‘yan bumburutu, kafa wuraren tace ɗanyen mai a cikin dazuka, ana haifar da gurɓacewar muhalli a ƙasar nan.
Tawagar wadda ke ƙarƙashin jagorancin Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ta ƙunshi Manyan Shugabannin Hafsoshin Ƙasar nan da kuma Ƙaramin Ministan Fetur, Heineken Lokpobiri.
Sauran mambobin sun haɗa da Ƙaramin Ministan Gas, Ekperipe Ekpo, Mashawarcin Musamman kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu da Shugaban NNPCL, Mele Kyari.
Sauran sun haɗa da Kwamandan Rundunar Sojojin Operation Delta Safe, Riya Admiral Olusegun Ferreira da sauran ɓangarorin jami’an tsaro.
Tawagar ta kai ziyara a Bututun mai na Owaza, Jihar Abiya, inda aka taras da an yi wani mahaɗar bututun mai da aka jona a asirce ana kwasar ɗanyen mai. Amma lokacin da tawagar ta isa wurin, an lalata jonin bututun.
“Za mu yi duk wani abin da zai kawo zaman lafiya a Neja Delta. A guji satar ɗanyen mai da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa.” Minista Badaru ne ya yi wannan gargaɗi da kuma shawara.
A nasa jawabin, Kyari ya ce za a riƙa gano masu satar ɗanyen mai ta ƙananan jiragen ruwa, amma sai da haɗin kan al’ummar yankin da ake haƙo ɗanyen man.
“Satar ɗanyen mai na daga cikin dalilin da ya sa Najeriya ba ta iya haƙo ɗanyen man da OPEC ta amince ta riƙa haƙowa a kullum,” inji Kyari.
Badaru ya jinjina wa jami’an tsaro da ma’aikatan NNPCL, kan rawar da su ke takawa wajen ƙoƙarin daƙile satar ɗanyen mai da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa.
Discussion about this post