Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja, Nysome Wike, ya sha alwashin cewa zai fatattaki duk masu kasa kaya gefen titi a cikin Abuja su na ‘yan saide-saiden kayayyaki.
Cikin wani faifan bidiyon da ke yawo a soshiyal midiya, an nuno Wike ya na cewa, “ba zan amince haka kawai a zo ana kafa laima gefen titi a cikin Abuja ba, ana wasu harkokin kasuwanci.
“Babban aiki na shi ne tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da bunƙasa Abuja. Ba a gina Abuja don a riƙa tallace-tallace da saide-saiden kayayyaki barkatai ba.
“Ina mamakin yadda za ka ga mutum ba a san daga inda ya ke ba, ya zo ya kafa ‘yar rumfar laima (umbrella) a gefen titi, wai ya na sayar da kayayyaki. To wannan barazana ce ga mazauna Abuja.
“Saboda irin su infoma ne na ‘yan fashi. Su na zaune ƙarƙashin ‘yar laima duk su na lura da shige-da-ficen masu gidaje. Ka na shiga gida sai dai ka ji sun kira ‘yan fashi, sun ce mutumin fa ya dawo, ya shiga gida yanzu.” Inji Wike a cikin bidiyon.
Ya ci gaba da cewa bai raina duk wani mai ƙaramar sana’a ba. To amma kuma ya ce don ka na ƙaramar sana’a dokar Abuja ba ta yarda ka zo ka riƙa takura wa mazauna birnin ko ka zama barazana gare su ba.
‘Masu Liƙa Hotuna Su Na Taya Ni Murna A Manyan Alluna Na Gode, Amma Su Daina’ – Wike
Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja, Nysome Wike, ya bayyana cewa a daina kashe kuɗaɗe ana taya shi murna ta hanyar yin tallace-tallace a manyan allunan Abuja.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Wike, Anthony Ogunleye ya fitar a Abuja, ya ce Minista Wike ya umarci a daina taya shi murna haka nan, kuma bai ce wani ya kashe kuɗi ya liƙa ɓarkeken hoton sa a manyan allunan Abuja ba.
Ya ce ya na godiya ga dukkan masu yi masa fatan alheri na kusa da na nesa. Ya ce amma a daina yi masa murna ana kashe makudan kuɗaɗe wajen tallace-tallace a manyan allunan Abuja haka nan.
Wike ya ce babban abin da ya sa gaba shi ne ci gaban babban birnin tarayya da kuma aiwatar da dukkan ayyukan da suka wajaba ya aiwatar, a matsayin sa na Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja.
Discussion about this post