Hukumar NiMET mai kula da yanayi ta yi kakkausan gargaɗin shirin ɓarkewar ruwan sama mai ƙarfi a jihohin Adamawa, Taraba, Benuwai, Ogun da Kuros Riba nan da kwanaki uku.
Haka kuma ana kyautata zaton zubar ruwa ba kamar na jihohin biyar, a Abuja da kewayen ta, Zamfara, Kebbi, Neja, Kwara, Ekiti, Osun, Oyo, Ondo, Edo, Kogi, Enugu, Nassarawa, Filato, Ebonyi, Imo, Abiya, Akwa Ibom, Bayelsa, Delta, Kaduna da Legas.
NiMET ta ƙara da cewa amma a sauran jihohin ba a hasashen samun ruwan a waɗannan kwanakin uku.
Sannan kuma sanarwar ta ce za iya fuskantar tsawa a lokacin da ruwan ya fara tsagaitawa.
“Akwai kuma yiwuwar a fuskanci iska mai ƙarfi a lokacin, a wasu jihohin da suka haɗa da Adamawa, Barno, Taraba, Yobe, Jigawa, Kano, Katsina, Kogi, Enugu, Kwara, Oyo, Ogun, Legas, Bayelsa, Edo, Ebonyi, Kaduna, Sokoto, Kebbi, Zamfara da kuma Nasarawa.”
A ƙarin gargaɗin da NiMET ta yi, ta ce iskan mai ƙarfi zai iya haddasa ɓarnar da ta haɗa da lalata gine-gine da kayar da bishiyoyi musamman a Arewacin Najeriya.
Discussion about this post