Tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya janye sha’awar sa na kasancewa cikin majalisar ministocin shugaba Bola Tinubu, kamar yadda binciken PREMIUM TIMES ya zakulo.
Majiyoyin mu daga fadar shugaban kasa sun bayyana mana cewa El-Rufai ya shaidawa shugaba Tinubu a waniganawa da suka yi a ranar Talata cewa ba ya sha’awar zama minista amma zai ci gaba da ba da gudummawar sa domin ci gaban Najeriya a matsayinsa na dan kasa.
“Ya kuma shaida wa shugaba Tinubu cewa yana bukatar lokaci don mayar da hankali kan karatunsa na samun digirin digir gir a wata jami’a Netherlands.”
Majiya ya shaida wa wannan Jarida cewa tsohon gwamnan ya ba da shawarar a nada wani makusancin sa minista, mai suna Jafaru Ibrahim Sani, yana mai cewa shugaban kasa zai same shimutum da za a yi tafiyar arziki da shi.
Sani ya taba zama kwamishina a ma’aikatu uku a jihar Kaduna (ilimi da muhalli na kananan hukumomi) yayin da El-Rufai ke gwamna.
Mun ji cewa tun bayan ya dawo Najeriya daga Landan, El-Rufai ya nemi ganawa da shugaban kasa, a wannan lokaci ya samu labarin kin tabbatar da shi da majalisar dattawa ta yi.
A ganawar, shugaban kasa Tinubu ya snara da El-Rufai cewa ya samu korafe korafe akan sa masu yawan gaske, da yana bukatar rana daya cur domin ya duba su dakyau sannan ya san wani mataki zai dauka.
A daidai wannan lokaci ne El-Rufai ya shaida wa Tinubu cewa, ya hakura da kujerar ministan, tunda kakara na ga ni kuma na ji a jikina akwai wasu zagaye da shugaban Kasa da basu so ya zama minista.
Duk da cewa El-Rufai ya ce, Tinubu ya bashi aikin soma bin diddigin yadda za a gyara harkar wutar lantarki a najeriya nan da shekara 7, kuma har ya fara aikin gadangadan, sai kuma ga korafi akan sa sannan shugaban kasa bai ce komai akai ba.
Discussion about this post