A ranar Juma’a darajar Naira ta ci gaba da zubewa a kasuwar ‘yan canji da dandamalin ‘yan zuba jari, inda a Abuja aka sayar da Dala ɗaya har Naira 950 a Abuja.
A Kano kuma wakilin mu ya tabbatar da cewa a ranar Juma’a Dala 1 ta kai Naira 960.
A wasu jihohi kamar Akwa Ibom kuwa, an sayar da Dala 1 kan Naira 940.
Darajar Naira na ci gaba da zubewa a daidai lokacin da farashin amfanin gona da kayan masarufi ke ƙara tsala wa marasa galihu, talakawa da masu ƙaramin ƙarfi bulala mai harshe uku.
Kayan da ake shigowa da su daga waje ma sai ƙara masu farashi ake yi a cikin birane da garuruwa.
PREMIUM TIMES Hausa a ranar Laraba, ta buga labarin cewa darajar Naira ta zube, ta doshi N1,000 a Dala 1.
Martaba da darajar Naira na ci gaba da zubewa a kasuwar ‘yan canji, ta yadda a ranar Laraba kaɗan ya rage a sayar da Dala 1 a Naira 1,000.
Amma a farashin daidaito na bankuna, an sayar da Dala 1 a Naira 782.38.
A kasuwannin ‘yan canji dai sai da Naira ta faɗi ƙasa har ta kai an canji Dala 1 a Naira 910, su kuma ‘yan canji su na saye Naira 905.
Tun bayan da Gwamnatin Tinubu ta saki Naira a kasuwa domin ta yi kiwo ba tare da makiyayin da ke kula da ita ba, a kullum duk gonar da ta ratsa sai ta ci dukan tsiya.
Sanadiyyar sakin Naira ba tare da linzami, tarnaƙi da dabaibayi a kasuwannin canjin kuɗi ba, tsadar rayuwa ta yi sama, malejin tsadar kayan masarufi ya cilla sama, haka duk wasu kayan da ake shigowa da su daga sai ƙara farashi su ke yi.
Hakan na zuwa ne daidai lokacin da ake fama da raɗaɗin tsadar rayuwa, biyo bayan cire tallafin fetur da Gwamnatin Bola Tinubu ta yi.
Tuni a kasuwannin yankunan karkara ake ci gaba da fuskantar tsadar kayan abinci, a gefe ɗaya kuma shiru ka ke ji, gwamnatin ta ƙi raba abincin tallafin da ta ce za ta raba.
Discussion about this post