Shugaban majalisar Dattawa ya bayyana cewa majalisar dattawa ba ta tabbatar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai kujerar minista ba saboda wasu dalilai da ke gaban hukumomin tsaro.
Idan ba’ a manta ba majalisa ta tantance El-Rufai domin zama minista a makon jiya.
Sai dai tun a lokacin da ake tantance tsohon gwamnan, ɗan majalisa daga jihar Kogi ya mika wasu takardu kunshe da korafe-korafe a kan sa.
Akpabio ya ce majalisa ba ta tabbatar da shi da wasu da aka tantance su uku, daga jihar Taraba da Jihar Delta saboda wasu korafe-korafe da aka mika game da su a majalisar.
” Muna jiran hukumomin tsaro su wanke su tukunna. Idan suka gama da su sai su miko mana rahoton su wanda da shine za mu tabbatar da su nan gaba.
Discussion about this post