Gwamna Muhammadu Inuwa-Yahaya na jihar Gombe ya bada odar a rufe gidajen tambaɗewa da holewa dake wasu sassan jihar.
Gwamnan ya kuma umarci dukkan jami’an tsaro da su tabbatar mutane sun kiyaye dokar.
Wannan sanarwa na kunshe ne a cikin wata takarda da sakataren gwamnati Ibrahim Abubakar-Njodi ya fitar a cikin wannan mako.
Njodi ya ce wannan matakin ya biyo bayan wasu koke-koke da mutane ke yi a kan fitsara da tambaɗewa da matasa da ƴan mata sula tsiri yi a jihar, kuma aka gano a waɗannan wurare ne ake aikata su.
Ya ce gwamnati ta umarci jami’an tsaro da suka hada da rundunar Sibul Difens, rundunar ‘yan sanda da rundunar ‘Operation Hattara’ su gaggauta tabbatar da ganin an kawo karshen wannan ayyukan fitsara da ake yi a wadannan wurare.
Waɗannan wurare sun haɗa da Jami’a Gidan Wanka dake Mile 3 layin Yola, Gombe, White House Theatre (Babban Gida) dake New Mile 3 layin Yola, Gidan Lokaci General Merchant dake Mile 3 hanyar Reservoir da Farin Gida Entertainment II a Wuro Karal layin Kalshingi.
Discussion about this post