Darajar Naira na ci gaba da zubewa a farashin gwamnati da kuma kasuwar ‘yan canji, yayin da a ranar Talata sai da Naira ta dangana an riƙa sayar da Dalar Amurka 1 kan Naira 799.90 a farashin gwamnati.
A ranar Litinini dai an rufe kasuwar canjin kan Dala ɗaya Naira 775.34, amma kuma a ranar Talata ta dangana zuwa Naira 799.90 duk Dala ɗaya, inda daga ƙarshe kafin tashi daga kasuwar hada-hadar kuɗaɗen.
A ranar Talata dai an yi musayar Dala miliyan 71.32 a kasuwar farashin gwamnati, wanda ake bai wa masu zuba jari.
A kasuwar ‘yan canji a Abuja kuwa, an yi cinikin duk Dala ɗaya kan Naira 910, a ranar Talata. Kusan hakan ne dai farashin ta a kasuwar ya kasance tun a ranar Litinin.
A kasuwar ‘yan canji ta Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom, an riƙa sayen Dala kan Naira 915, su kuma su ka riƙa sayarwa kan Naira 920.
A ranar Litinin kuwa, Naira 913 aka sayar da Dala a Uyo.
Wani rahoton PREMIUM TIMES cikin makonni biyu suka gabata, ya tabbatar da cewa, fargabar faɗuwar darajar Naira ta sa Shugaba Bola Tinubu ya gana da Gwamnan CBN a gaggauce.
Shugaba Bola Tinubu ya fara razana ganin yadda darajar Naira ke ci gaba da zubewar da ba ta taɓa yi ba a duniya.
Wannan razanar ce ta kai shi ga yin ganawar gaggawa a Shugaban Babban Bankin Najeriya, Folashodun Sonubi a ranar Litinin.
Sun yi ganawar ce ganin yadda Naira kaɗan ta rage ta kai N1,000 ke daidai da Dala 1 a kasuwar ‘yan canji, yayin da a kasuwar hada-hadar zuba jari kuwa, ta doshi Naira 800 a dala ɗaya.
A wurin taron dai su biyun sun tattauna yadda za a farɗaɗo da Naira a kasuwa, yadda idan ta na tafiya ba sai ta riƙa dogara sanda ko ana yi mata tatata ba.
Bayan kammala taron Shonubi ya shaida wa manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa cewa, “Shugaban Ƙasa ya damu ƙwarai da halin da Naira ta tsinci kan ta.”
Sai dai shi kuma ya ce ya yi amanna faɗuwar darajar Naira ba don yawan neman ta ne da ake yi ba, sai kawai saboda ci gaba da saɓat-ta-juyat-tar da ake yi wa dala a kasuwannin ‘yan canji.
A ranar Asabar ce PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Naira ta kama hanyar yin abota kafaɗa-da-kafaɗa da takardar tsire da balangu.
A ranar Juma’a darajar Naira ta ci gaba da zubewa a kasuwar ‘yan canji da dandamalin ‘yan zuba jari, inda a Abuja aka sayar da Dala ɗaya har Naira 950 a Abuja.
A Kano kuma wakilin mu ya tabbatar da cewa a ranar Juma’a Dala 1 ta kai Naira 960.
A wasu jihohi kamar Akwa Ibom kuwa, an sayar da Dala 1 kan Naira 940.
Darajar Naira na ci gaba da zubewa a daidai lokacin da farashin amfanin gona da kayan masarufi ke ƙara tsala wa marasa galihu, talakawa da masu ƙaramin ƙarfi bulala mai harshe uku.
Kayan da ake shigowa da su daga waje ma sai ƙara masu farashi ake yi a cikin birane da garuruwa.
PREMIUM TIMES Hausa a ranar Laraba, ta buga labarin cewa darajar Naira ta zube, ta doshi N1,000 a Dala 1.
Martaba da darajar Naira na ci gaba da zubewa a kasuwar ‘yan canji, ta yadda a ranar Laraba kaɗan ya rage a sayar da Dala 1 a Naira 1,000.
Amma a farashin daidaito na bankuna, an sayar da Dala 1 a Naira 782.38.
A kasuwannin ‘yan canji dai sai da Naira ta faɗi ƙasa har ta kai an canji Dala 1 a Naira 910, su kuma ‘yan canji su na saye Naira 905.
Tun bayan da Gwamnatin Tinubu ta saki Naira a kasuwa domin ta yi kiwo ba tare da makiyayin da ke kula da ita ba, a kullum duk gonar da ta ratsa sai ta ci dukan tsiya.
Sanadiyyar sakin Naira ba tare da linzami, tarnaƙi da dabaibayi a kasuwannin canjin kuɗi ba, tsadar rayuwa ta yi sama, malejin tsadar kayan masarufi ya cilla sama, haka duk wasu kayan da ake shigowa da su daga sai ƙara farashi su ke yi.
Hakan na zuwa ne daidai lokacin da ake fama da raɗaɗin tsadar rayuwa, biyo bayan cire tallafin fetur da Gwamnatin Bola Tinubu ta yi.
Tuni a kasuwannin yankunan karkara ake ci gaba da fuskantar tsadar kayan abinci, a gefe ɗaya kuma shiru ka ke ji, gwamnatin ta ƙi raba abincin tallafin da ta ce za ta raba.
Discussion about this post