Wani abinda yake ci min tuwo a kwarya shine yadda kungiyar kwadago suka zama sun fi son kan su fiye da mutanen Najeriya. A kullum suka fita kalubalantar wasu manufofin gwamnati za ka ga karshe dai a aljihun su abin yake komawa. Talaka ko oho.
Duk da cewa Talaka a Najeriya yanzu na dandana kudar sa wajen tsadar abinci da ma rayuwa baki daya, abinda ya fi dacewa shine kungiyar Kwadago su matsa wa gwamnatin tarayya domin ta tabbatar da cika alkawuran da ta dauka tun bayan cire tallafin amin fetur amma ba kirkiro sabuwar wahala ba ta tsinduna yan Najeriya a ciki, ba su ji ba basu gani ba.
Shugaban Kasa Bola Tinubu a jawabin sa ya ayyana cewa tallafi da shirye shirye da gwamnati ta tsaro masu hahimmanci na tafe, kuma abinda gwamnati ta maida hankali a kai kenan yanzu. Ni a ganina shine a ba gwamnati lokaci tukunnan zuwa kofda wata uku ne aga kamun ludayin ta da kyau, amma ab kawai kuma kungiyar Kwadago ta bijiro da wani sabuwar wahala ta ingiza ‘yan najeruya a ciki.
Wannan kiraye kiraye na soma yajin aiki da kungiyar Kwadago ke yi ba zai yi tasiri ba saboda yanayin rayuwa da ake ciki. Wannan yanayi ba zai sa mutane su iya biye wa kungiyar ba har su fito domin yin wannan zanga zanga.
Gawurtattun ‘yan siyasa da masu harkallar mai da cire tallafin ya kawo wa cikas sune ke ingiza kungiyar da kuma tilasta sai gwamnati ta dawo da tallafin domin aljihun su sun fara bushewa. Maimakon a hadu ne a nuna wa gwamnati, ta gaggauta samar da tallafi musamman a fannin motocin sufuri, karya farashin abinci da sauran kayan masarufi domin talaka amma su a na su tunanin idan aka dawo da tallafin man shine talaka zai more.
Buhun Shukafa dai tun kafina cire Tallafin Mai ya kai kusan naira 40,000, har yanzu kudin sa kenan watanni biyu bayan cire tallafin.
A dai duba a yi nazari, kada kuma maimakon talaka ya samu sauki, a dada jefa shi cikin halin kakanikayi.
Discussion about this post