Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta jihar Bauchi (BASPHCDA), Rilwanu Mohammed ya bayyana cewa cutar Diphtheria ta Yi ajalin mutum 26 a jihar.
Mohammed ya fadi haka ne a taron da Asusun USAID ta shirya da aka yi a garin Bauchi ranar Alhamis.
Ya ce sakamakon gwajin da aka gudanar ya nuna cewa mutum hudu sun mutu a dalilin kamuwa da cutar sannan sauran mutum 22 sun mutum saboda wasu alamun cutar da suka fara nunawa a jikinsu.
“Zuwa yanzu muna zargin mutum 180 sun kamu da cutar a kananan hukumomin Bauchi, Dambam 32, Darazo 2, Itas Gadau 5, Jamaáre 104, Katagum 17, Misau 9, Ganjuwa 1, Giade 1 da Ningi 1.
“Sakamakon gwaji ya tabbatar cewa mutum 7 sun kamu da cutar, mutum 166 na nuna wasu alamu dake kama da na cutar daga cikin mutum 180 din da muke zargin sun kamu.
“Akalla mutum daya ya kamu da cutar a kananan hukumomi 10 dake jihar sannan mutum 57 sun kamu da cutar a karamar hukumar Jama’are.
“Cutar ya kama mutane masu shekaru daga daya zuwa 55.
“Asibitin kula da masu fama da cutar na karamar hukumar Jama’are inda cutar ta fi yaduwa a jihar.
Gwamnan jihar Bala Mohammed ya bai wa fannin kiwon lafiyar jihar da ta yi gaggawan daukan matakai domin ganin sun dakile yaduwar cutar a jihar Bauchi.
Idan ba a manta ba a watan Yuli PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda Diphtheria ta bullo a kananan hukumomi shida a jihar Bauchi.
Hukumar BASPHCDA ta ce mutum uku ne suka kamu da cutar inda mutum biyu daga cikin uku sun mutu a karamar hukumar Jama’are.
A lokacin hukumar ta gano wani dan karamin yaro mai shekara bakwai da ya kamu da cutar sannan yara kananan da makiyaya musamman wadanda basu Yi allurar rigakafi ba na daga cikin wadanda suka fi kamuwa da cutar.
Hukumar ta ce gwamnati ta rufe duk makarantun bokon dake karamar hukumar Jama’are sannan za ta zage damtse wajen yi wa yara allurar rigakafi musamman a karamar hukumar Jama’are.
Ga abubuwa 9 game da cutar Diphtheria
1. Menene cutar Diphtheria
Cutar Diphtheria cuta ce da kwayoyin cutar bacteria mai suna ‘Corynebacterium’ ke haddasa wa.
Babu babba ko yaro a yadda Cutar ke yaduwa amma jami’an lafiya sun ce cutar ya fi kama yara kananan musamman wadanda ba su yi allurar rigakafin cutar ba.
2. Hanyoyin kamuwa da cutar.
Ana iya kamuwa da cutar ta hanyar sumba musamman idan ana yin sumban da mutane daban-daban.
Cutar na yaduwa idan ana yawan zama kusa da masu fama da cutar.
Idan mai dauke da cutar ya yi tari ko atishawa ba tare da ya rufe bakinsa ba.
Sannan da yawan yin amfani da kayan da masu fama da cutar suka yi amfani da su kamar chokali, Kofi, hakichin da sauran su.
3. Mutanen da suka fi kamuwa da cutar
Cutar Diphtheria ya fi kama yara da manya musamman wadanda tun farko ba su Yi allurar rigakafin cutar suna yara ba sannan da kin yin allurar rigakafin yayin da suka girman.
4. Alamun cutar
Akan gane alamun cutar bayan ranar farko zuwa rana ta 10 bayan kamuwa da cutar.
Alamun cutar sun hada da zazzabi, yoyon hanci, ciwon makogwaron, idanun za su Yi jajawur, tari da Kumburin wuya.
Wasu lokuta mai fama da cutar zai rika ganin wasu farin abubuwa na fitowa da a kusa da makogwaron sa wanda ke hana mutum iya yin numfashi da hadiyan abinci.
5. Abin da ke haddasa cutar
Kwayoyin cutar ‘Corynebacterium diphtheria’ ne ke haddasa cutar inda yakan kama hanci, makogwaron da fatara mutum.
Rashin tsaftace muhalli na haddasa cutar
6. Ire-iren cutar Diphtheria
Cutar diphtheria ya rabu biyu inda akwai ‘Classic respiratory’ wanda kan kama hanci makogwaro sannan da ‘Cutaneous’ wanda kan kama fatar mutum.
7. Hanyoyin gane cutar a jikin mutum
Jami’an asibiti na iya gano cutar daga alamun kamuwa da cutar da suka fara nunawa a jikin mutum kokuma idan aka Yi wa mutum gwajin cutar.
8. Maganin cutar
Wanda ya kamu da cutar zai killace kansa sannan maganin ‘Antibiotices’ na kawar da cutar daga jikin mutum.
Sannan ruwan dumi akai-akai na taimakawa wajen rage zafi da Kumburin makogwaro.
Hanyoyin guje wa kamuwa da cutar
A. Yin allurar rigakafi.
B. Saka takunkumin fuska musamman idan za a shiga cikin mutane.
C. Kare baki da hanci idan za a yi tari ko atishwa.
D. Tsaftace muhalli, wanke hannu da ruwa da sabulu a kowani lokaci.
E. Zuwa asibiti da zaran an kamu da zazzabi ko idan ba a gane lafiyar jiki ba
Discussion about this post