Mazauna garuruwan dake dake da iyaka da Najeriya da Nijar a yankin Karamar hukumar Jibiya, Jihar Katsina sun afka cikin tsananin matsi na wahalar rayuwa a sanadiyyar rufe iyakar kasar Nijar da gwamnatin Najeriya ta yi, wanda hakan na daga cikin zartaswar kungiyar ECOWAS.
Idan ba a manta ba, gwamnatin Najeriya ta rufe Iyakokin ta da kasar Nijar Nijar a sanadiyyar juyin mulki da wasu sojoji suka yi a kasar.
PREMIUM TIMES ta yi tattaki har zuwa wasu da ga cikin garuruwan da ke karamar hukumar jibiya domin tattaunawa da mazauna wadannan garuruwa da kuma sanin halin da suke ciki.
Saidu Bala ya shaida wa wakilin mu cewa tabbas mutane sun afka cikin mawuyacin hali a dalilin rufe bodar da aka yi.
” Mu da mutanen Nijar fa kusan duka gari daya ne. rufe boda ya ka wo mana tsananin talauci da damuwa a tsakanin mu. Na kan samu naira 20,000 duk rana a aikin acaba da nake yi daga nan zuwa cikin Nijar. Amma yanzu babu mu na zaune ne hannu rabbana.
Discussion about this post