Tsohuwar Ministar Harkokin Fetur a zamanin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, za ta fuskanci tuhuma a kotun Landan, lamarin da kan iya kai ga ɗaure ta, kamar yadda aka ɗaure tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu a birnin Landan.
Diezani mai shekaru 63, wadda har shugabancin OPEC ta yi, ta yi sharafi a Gwamnatin Najeriya, tsakanin 2010 zuwa 2015.
Mahukuntan Birtaniya na zargin cewa ta karɓi rashawa lokacin da ta ke Ministar Harkokin Fetur a Najeriya, wurin bayar da kwangilolin maƙudan miliyoyin kuɗaɗe, a kwangilar fetur da gas.
Ana kuma zargin ta karɓi fam na Ingila 100,000, zunduma-zunduman motoci, ɗaukar nauyin yi mata shatar jiragen sama, tafiya hutun ɓalle-bushasha kyauta, ita da iyalin ta.
Ana kuma zargin ta da amfani da manyan kadarori masu yawa a birnin Landan, inda take gudun hijira, tun bayan hawan tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, cikin 2015.
Hukumar Hana Aikata Manyan Laifuka ta Birtaniya (NCA) ce ta kammala bincike-binciken da hukumomi suka yi kan Diezani.
Ana kuma zargin ta karɓi kyautar kayan ɗaki na alfarma, an yi mata gyaran gida kyauta a matsayin cin hanci, kuma an riƙa biya wa kuɗaɗen makarantar yaran ta. Akwai kuma zargin karɓar kyauta daga katafaren kantin sayar da kayan ƙwalisa na duniya, wato Cartier, inda aka ba ta kyautar sarƙa da awarwaro masu tsadar wuce hankali.
Haka nan kuma an ba ta irin waɗannan kyautar a katafaren kantin ƙwalisa na Louis Vuitton.
Diezani, wadda a yanzu haka ke zaune a unguwar St John’s Wood, Landan, za ta bayyana a gaban kotu a ranar 2 Ga Oktoba, a gaban Mai Shari’a na Kotun Majistare da ke Westminster.
Shugaban Hukumar Hana Aikata Manyan Laifuka (NCA), Andy Kelly, ya bayyana cewa laifukan da ake zargin Diezani ta aikata, abin ƙyama ne matuƙa.
Cikin watan Maris na wannan shekarar sai da NCA ta aika wa Ma’aikatar Shari’a ta Amurka bayanan wata daƙa-daƙa da ƙada-ƙadar da Diezani ta afka a Amurka. Hakan ya sa an gano wasu maƙudan kuɗaɗe har Dala Miliyan 53.1 da ta ɓoye a can, waɗanda aka tabbatar kuɗaɗen na cuwa-cuwa da gada-gada ne.
Discussion about this post