Wani makiyayi Ɗan shekara 15 mai suna Adamu Ibrahim ya guntule hannun hagun wani manomi yayin rikici da ya shiga tsakanin su ranar Asabar a jihar Bauchi.
Lamarin ya faru ne a kauyen Jital da ke kan titin Gombe. Ana zargin makiyayin ya kutsa da shanu sa cikin gonar shinkafar wannan manomin ne.
A cewar rundunar ƴan sandan bayan da makiyayin ya kutsa cikin gonar, sai faɗa ya ɓarke a tsakanin su, wanda ya kai ga guntule hannun manomin.
An garzaya da manomin zuwa Asibitin Koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) Bauchi, inda a halin yanzu yake jinya.
Sai dai kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Ahmed Wakili, ya shaida wa manema labarai a ranar Asabar cewa, ƴan sandan na ci gaba da bincike kan lamarin.
Ya ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa wanda ake zargin na da dabi’ar kutsawa cikin gonakin manomin da shanunsa tare da lalata masa amfanin gona.
Wakili ya ce sau da dama manomin ya kai kara wurin mahaifin wannan makiyayin da ake zargi, amma hakan bai hana shi shiga gonar manomin da shanu sa tare da lalata amfanin gonar ba.
Binciken ya kuma nuna cewa, a ranar 24 ga watan Agusta, 2023, wanda ake zargin, dauke da sanda da adda, ya yi wa manomin ɓarna a gonar manomin.
“Don haka ne aka samu rashin jituwa, inda wanda ake zargin ya yi amfani da addar sa mai suna Sharpe ya guntule wa manomin hannu.
Yanzu dai makiyayin na tsare hannun ƴan sanda.
Discussion about this post