• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Ƴan sanda sun damke wasu abokai ƴan kungiyar matsafa dake tsafi da kawunan mutane a Ilori

    Yadda ƴan sanda suka kama Ibrahim da ya yi garkuwa da Fatima, ya ƙarɓi kuɗi kuma ya yashe ta a Zariya

    Kotu ta kori gwamna Sule na Nasarawa, ta ce PDP ce ta yi nasara a zaɓen gwamna

    Ku fito ku ceci mutanen jihar Kaduna kamar yadda kuka yi a zaben majalisun Tarayya da na sanatoci – Isah Ashiru

    An yi mana kwange a hukuncin kotu, za mu daukaka kara – Ashiru

    SSS

    TAKE HAƘƘIN ƊAN ADAM: Yadda SSS suka riƙa faffalla min mari, suka ja ni ƙasa girrrr, don kawai na ce su bi doka – Lauya Ogbankwa

    Muna ƙarancin malamai, a janye dokar hana ɗaukar sabbin malamai da gwamnatin tarayya ta ƙaƙaba – Jami’ar ABU

    TONON ASIRI: An kama wani Dagaci cikin gungun mahara a lokacin batakashi da ‘Yan sanda

    ‘Yan bindiga sun kashe mutum shida a Kaduna

    Almajirai

    UNICEF ta saka Almajirai sama da 20,000 cikin rajistar tsarin agaza wa marasa karfi a Katsina

    Majalisar Tarayya ta ce a soke ƙarin kuɗin makaranta da aka yi wa ɗaliban jami’o’i da na Kwalejojin Gwamnatin Tarayya

    KALUBALEN DA KE GABAN MAJALISAR WAKILAI TA ƘASA: Gaganiya da matsalar raɗaɗin tsadar rayuwa, matsalar tsaro da sauran su da ake fuskanta a kasa

    Yadda sojojin sama sun ragargaza sansanonin ‘yan bindiga a jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto da Kaduna

    RASHIN TSARO: Tinubu ya amince da sayo jiragen sama masu saukar ungulu 12 ga sojojin Najeriya – Lagbaja

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    Hukumar CAF za ta binciki yadda mahaifiyar ɗan wasa ta mutu cikin 1986, shi kuma ya ce atabau cikin 1990 ta haife shi

    A karo na Uku, Moroko za ta ɗauki baƙuncin gasar cin kofin kwallon ƙafa na nahiyar Afrika a Janairun 2025

    NFF ta sake nada Chris Danjuma a matsayin kocin Falconets

    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    BIDIYO: Yadda rufe iyakar Najeriya da Nijar, ya jefa mu cikin tsananin fatara, da halin kakanikayi a yankin Katsina – Saidu

    Yadda SSS da Jami’an Gidan Kurkuku suka kwashi ‘yan kallo a kotu, saboda Emefiele

    BIDIYO: ‘Duk wanda ya ci kuɗin Tallafin Korona a Jigawa sai ya amayo shi’ – Gwamna Namadi

    BIDIYO: ALhazan Kano sun gama shiri tsaf don ‘Hawan Arafat’ – Alhussain Maiwada

    JERIN SUNAYE: Jami’o’i 51 da ba za su dauki dalibin da ya ci kasa da maki 180 a jarabawar JAMB ba

    TSARIN BAI WA ƊALIBAI RAMCE: Abubuwan da suka wajaba ɗalibai da iyaye su sani

    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

No Result
View All Result

BATUN BADA BELIN EMEFIELE: ‘Abin da ya sa har yau ba mu bi umarnin kotu ba’ – Gwamnatin Tarayya

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
August 16, 2023
in Manyan Labarai
0
Yadda kotu ta ƙi bai wa SSS sammacin iznin shaƙo wuyan Gwamnan CBN

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa wasu ƙa’idoji na gwamnati da kuma wasu canje-canjen zargin da ake wa tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya sa har yau ba a sallame shi bayan kotu ta bayar da belin sa ba.

Daraktar Shigar da Ƙararraki a Ma’aikatar Harkokin Shari’a, Abubakar Mohammed ne ya bayyana haka ga manema labarai, bayan tashi daga zaman kotu a kan Emefiele, a ranar Talata.

Ya je kotun ne domin ya nemi janye tuhumar mallakar bindigar da ake yi wa Emefiele, daga nan kuma a sake shigar da wasu tuhume-tuhume a kan sa, duk dai can a Babbar Kotun Tarayya da ke Ikoyi, Legas.

Mohammed ya ƙara da cewa sake kama Emefiele da aka yi a cikin harabar kotu, bai nuna cewa an bijire wa umarnin kotu ba.

Ya ce baya ga batun sai ya cika sharuɗɗan beli, to akwai kuma wani bincike da ake yi masa kan wasu laifuka da ya tafka, waɗanda sai an kammala sannan za a san irin tuhumar da zai fuskanta.

“Kuma a yanzu haka akwai wata tuhumar da ake yi masa a Babbar Kotu. Saboda waɗannan su ne su ka taru su ka haifar da tafiyar-hawainiyar da ake yi a batun belin Emefiele, amma ba ƙin bin umarnin kotu ne Gwamnatin Tarayya ta ƙi yi kai-tsaye ba.”

Sai dai kuma Lauya Monday Ubani ɗan rajin kare haƙƙin jama’a, ya ce dalilan da gwamnatin tarayya ta bayar ba abin yarda ba ne, domin ita kan ta kotu ta ce hutumar da ake wa Emefiele, wadda ake bayar da beli ce.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Gwamnatin Tarayya za ta janye tuhumar mallakar bindigar da ta ke wa Godwin Emefiele.

A labarin, Gwamnantin Tarayya ta sake garzayawa kotu a ranar Talata, ta na neman ta janye tuhumar mallakar bindigar da ta ke wa tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Ta bayyana aniyar neman tuhumar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas.

Daraktan Gurfanar da Waɗanda Ake Zargi na Gwamnatin Tarayya, a Ma’aikatar Shari’a, Abubakar Mohammed ne ya sanar wa kotun haka, a ranar Talata, yayin da ya ke magana da baki, ba a rubuce ba a gaban kotun.

Ya shaida wa Mai Shari’a Nicholas Oweibo hakan bisa dalilin wasu ƙarin abubuwan da Gwamnatin Tarayya ta binciko kan Emefiele.

Bayan fitowa daga kotu, Mohammed ya shaida wa manema labarai cewa, “Gwamnatin Tarayya ka iya dawowa kotu da ƙarin canje-canje a kan Emefiele.”

Zargin Mallakar Bindigar Da Gwamnatin Tarayya Ta Janye Kan Emefiele:

Zargin Mallakar Bindiga: Kotu ta bada belin Emefiele, ta ce bai aikata laifukan da za a ci gaba da tsare shi ba.

Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta bada belin tsohon Shugaban Babban Bankin Najeriya,
CBN, Godwin Emefiele.

SSS sun gurfanar da shi a ranar Talata, shi ne
lauyan sa ya ce a ba shi beli.

Mai Shari’a ya ce za a iya belin Emefiele a kuɗi ₦20,000,000.00.

SSS sun gurfanar da Emefiele kotu, a madadin Gwamnatin Tarayya, ta gurfanar da tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Emefiele a kotu.

SSS sun maka shi Babbar Kotun Tarayya, inda ake zargin sa da mallakar
bindiga da harsashe.

An gurfanar da shi a ranar Alhamis, amma ba a sa ranar da za a fara shari’ar ba.

Ana tsare da shi tun a ranar 10 Ga watan da ya gabata, har kotu ta yi gargadi a sallame shi Ko a gurfanar da shi.

Sai dai kuma maimakon a ga zargi da ake yi masa da ta’addanci da farko, ya ana tuhumar sa da mallakar hargitsa bindiga da harsashi.

Babbar Kotun Tarayya ta ce wa SSS ‘Ku gurfanar da Emefiele a kotu, ko ku sake shi.’

Babbar Kotun Tarayya ta gargaɗi SSS cewa su gaggauta sallamar tsohon Gwamnan ta saɓa doka ce ƙarara.

Lauyoyin sa su ka garzaya kotu domin su yi bayani cewa SSS sun toshe hanyoyin ganawa da Emefiele ɗin.

Bayan kama shi, wasu ‘yan raji su ka ce EFCC da ICPC ke da alhakin su kama Emefiele, amma ba aikin SSS ba ne.

Cikin su har da tsohon Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA), ya bayyana abin da ya kira “damuwar sa”, dangane da kamun da Hukumar Tsaro ta SSS ta yi wa dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Agbakoba ya ce babu wani ƙorafi don an dakatar da Emefiele, amma dai shi bai ga dalilin da zai sa SSS su kama shi ba, tunda su dai babu ruwan su da shiga lamarin laifukan da su ka shafi harkokin tattalin arziki ko kuɗaɗe.

“Aikin SSS shi ne tabbatar da tsaron cikin gida, wato cikin ƙasa. To me zai kai su ga kama Emefiele?

“Abin mamakin shi ne yadda sauran hukumomin da ke da haƙƙin binciken harkokin zambar kuɗaɗe su ka yi shiru, har yau ba su ce komai ba dangane da Emefiele, tun bayan dakatar da shi. Sai kawai ji mu ka yi SSS sun ce ya na hannun su. In dai ba zargin aikata zagon ƙasa ga gwamnati ba, me zai kai SSS su kama shi?” Inji Agbakoba.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin kama Emefiele da SSS yi, sannan aka jefa shi magarƙama bayan Tinubu ya dakatar shi.

A cikin labarin kuma an bayyana yadda SSS su ka zarge shi da laifin taimaka wa ‘yan ta’adda da kuɗaɗe, amma kotu ta hana kama shi a cikin Disamba, saboda rashin ƙwaƙƙwarar hujja.

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (SSS) ta bayyana cewa ta kama dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele.

DSS sun kama shi, ba da daɗewa ba bayan Gwamnatin Tarayya ta bayar da sanarwar dakatar da shi.

Sanarwar da damƙe Emefiele ta fito daga bakin Kakakin Yaɗa Labaran SSS, Peter Afunanya, a cikin wata sanarwar manema labarai da ya raba, ya aiko wa PREMIUM TIMES.

Idan ba a manta ba, cikin watan Disamba, 2022 SSS sun nemi kama shi domin zargin ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda, amma kotu ta hana su, saboda rashin ƙwaƙƙwarar shaida.

Tags: AbujaEmefieleHausaLabaraiNewsPREMIUM TIMES
Previous Post

ALƘAWARIN TINUBU GA ‘YAN NAJERIYA: ‘Ba za a sake ƙara farashin fetur ba’

Next Post

‘Yan sandan Kano sun kama barayin waya, ‘Yan Kwalewa da tantiran batagari 1000 a sassa daban-daban na jihar

Ashafa Murnai

'Yan sandan Kano sun kama barayin waya, 'Yan Kwalewa da tantiran batagari 1000 a sassa daban-daban na jihar

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Yadda ƴan sanda suka kama Ibrahim da ya yi garkuwa da Fatima, ya ƙarɓi kuɗi kuma ya yashe ta a Zariya
  • Kotu ta kori gwamna Sule na Nasarawa, ta ce PDP ce ta yi nasara a zaɓen gwamna
  • Gwamnatin Tinubu ta sanar da dakatar da harajin (VAT) kan man dizal na tsawon watanni 6
  • Matsayar da aka cimma a taron Gwamnatin Tarayya, NUC da TUC – Minista Idris
  • ‘Gyaran Najeriya sai a hankali, miji na ba da rauhanai ya ke aiki ba’ – Remi Tinubu

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.