Rundunar ‘yan sandan Ondo ta kama wani mutum mai shekaru 45 Bankole Oginni bayan an tsinci gawar budurwarsa a dakinsa.
Sakamakon bincike‘yan sanda ya nuna cewa mamaciyar tsohuwar budurwar Oginni ne kuma ta rasu tana da shekaru 45 tana da ‘Ya daya.
Jami’an tsaro sun ga kunar wuta a jikin matan sannan an fafe cikin ta babu hanji, ba Koda, ba hanta ba tumbi.
Kakakin rundunar Funmilayi Odunlami ta ce ‘yar matar ne ta kawo kara a ofishin ‘yan sandan bayan ta ga gawar mahaifiyar ta a gidan Oginni dake Oke Aro a Akure ranar Lahadi.
“’Diyar matar ta ce a ranar Lahadi mahaifiyar ta ta fice da gida ta nufi gidan tsohon saurayinta Oginni. Ta ce har zuwa yamma mahaifiyarta ba ta dawo gida ba sannan wayoyinta duka a kashe.
“Daga nan ne yarinyar ta je gidan tsohon saurayin mahaifiyar ta inda ta ga gawar ta an daure hannu da kafafunta sannan cikinta a fafe, babu komai a ciki sai fatan jiki.
Funmilayi ta ce Oginni na tsare a ofishin su sannan rundunar ta fara gudanar da bincike a kai.
Discussion about this post