Ga dukkan alamu fa, wahala bata kare ba, kuma babu ranar wucewar ta a nan kusa, ‘Yan Nijeriya mu shirya rungumar kaddara. Ita dama kaddara a kwai wadda Allah ya kan kawo ta domin jarabar bayin sa, ko kuma sakayyar yi gangancin su, wajen damar da suka samu na yiwa kan daidai ko akasin hakan.
Ita kyakkyawar Juma’a tun da ga Laraba a ke gane ta, alamu kan nuna yiwuwar kyawun al’amari a farkon sa, tun kafin a yi nisa. Shi mutum ya sha babban ne da dabba, domin yin amfani da hankalin da ilimin da Allah ya hore masa, wajen nazartar abin da ke gaban sa don hango abin da ke gaba da shi ko mai zuwa.
Jawabin Shugaba Tinubu da yiyi wa ‘Yan Nijeriya ranar 31 ga watan July da kuma yin nazarin da irn mutane da ya mikawa Majalisar Dokoki ta Kasa, domin tantancewa, don nadasu Ministocin kuma mambobin Majalisar Zartarwa ta Kasa, zamu iya nazartar irin takarawar da wannan gwamnatin zata yi.

Dama kuma ‘Yan Nijeriya fa suna cikin tsananin rayuwa tun a mulkin baya na Shugaba Buhari, sai gashi matakin da ita wannan gwamnatin ta Shugaba Bola Tinubu na cire tallafin man-fetur, da kuma matakin gwamnatin na ragewa Naira daraja a kan Dallar Amurka, sun yi bazata wajen kara saka mutane Nijeriya cikin tsananin rayuwa fiye da baya, kuma da dukkan alamu, ita ma wannnan gwamnati tazo, babu kintsattsen shiri na ko ta kwana ga ‘Yan Nijeriya a yanayin da suke ciki a yanzu. Wanda dama a nazari na tattalin arziki, a kwai harsashen tashin kayan bukatu na yau da kullum da kuma yiyuwar karuwar talauci a wajen yan kasar.
JAWABIN SHUGABA TINUBU DA YANAYIN DA YAN KASA SUKE CIKI
Ko shakka babu, in a ka yi nazari a kan jawabin Shugaba Tinubu game da tsare tsaren sa, na fasalta tattalin arzikin Nijeriya da kuma tsarin sa na kawo wa Yan Nijeriya saukin rayuwa, zai kasance kamar karatun labari ne irin wanda tsohon shugaba Buhari ya sha yi, ba tare da ganin canji ba.
In a kayi duba da irin tanade tanade da a ka ce za a yi wa ‘Yan Nijeriya, kusan babu irin wanda gwamnatin ba ta yi ba, amma babu wata gagarumar nasara, wajen canja rayuwar ‘yan Nijeriya.
Bayar da bashi ga manyan masana’antu, ita kanta gwamanti Buhari ta bawa Masana’antun sarrafa maganunuwa na Kasarnan bashin da yakai naira biliyan dari N100B ta hannun babban bankin kasa (CBN).
Ko da kananan ‘yan kasuwa da manoma da Shugaba Tinubu yace za a tallafawa da bashi don fita daga wannan radadin, babu wani abu da zai chanja. Domin gwmantin Buhari da ta gabata ta bayar da bashin da ya wuce naira biliyan dubu dari biyu (N200B) ga kimanin kananan yan kasuwa miliyan da dubu dari biyar (1.5m). Shin wane irin chanji ya nuna ga rayuwan yan Nijeriya?
Kai hatta kananan masana’antu, gwamnatin Buhari daga shekara ta 2017 zuwa 2023 ta raba musu bashin da yakai naira biliyan dari (N100B) ta bankin ci gaba na kasa (DBN).
Game da bayar da takin zamani domin bunkasawa da rage radadin talauci ga manoma, ya kamata a bibiyi ‘Presidential Fertilizer Initiative’ na tsohon shugaban kasa Buhari, domin gudun yin takon kwaba.Koda maganar samar da motocin sufuri da kuma yin amfani da man diesel mai sauki, ita ma wannan dabarar Shugaba Buhari ya gwada ta amma ba ta je ko ina ba.
In dai wadannan ne tanade tanadan wannan gwamnati, to gasakiya Shugaba Tinubu shima kamar Shugaba Buharin kenan yake, domin mun jira muji tsare tsare da manufofi sabanin na baya da bawa mutane kwarin gwiwar samun canji, musamman a yanayin halin da suke ciki.
SABBIN ‘YAN MAJALISAR ZARTARWA (MINISTOCI)
Ita ma fa wannan gwamnati ta Tinubu kamar wadda ta gada ta Buhari ta dau tsawan lokaci kafin gabatar da sunayen ministocin, duk da kasancewar gyaran doka da kaiwa Majalissa sunayen su kafin kwana talatin da rantsar da shugaban kasa, wanda har yanzu ba a gama kaiwa sauran mutanen ba.
Duk da wannan tsawan lokaci, sai ga shi jerin sunayen da Shugaba Tinubu ya zakalo don nadasu ministoci, tamkar gauraya tsimin da ya kwana ne. Domin tarun sunayen da suke ciki, walau tsofin gwamnoni ne da suka yi mulki tare da Shugaba Buhari, wasu kuma sun rike mukamai a gwamnatin da ta gabata, kusan duk tsare tsare da kuma gudanarwar gwamnatin baya da su aka yi.
In har ba shi Shugaba Tinubun ne ke da wani jadawali nasa ba, to zai yi wahala ta chanza zani a rawar da shi Tinubun zai taka don kaiwa Nijeriya gaba.
In har ba a yi dace ba fa, ‘Yan Nijeriya su shirya da karba kaddara, domin da wuya a samu chanjin da a ke fata samu a kusa, har yanzu dai, akwai alamun sauran wahala.
alhajilallah@gmail.com
Discussion about this post