Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa (NEC), ta yi tsokacin cewa akwai buƙatar a riƙa taka-tsantsan wajen ririta kuɗaɗen shigar da Najeriya ke samu.
A taron ta na 135, wanda ta gudanar a ƙarƙashin Mataikakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, NEC ta ya kamata a riƙa fayyace adadin kuɗaɗen da ake tarawa bayan cire tallafin fetur, sannan kuma a riƙa tantance abin da aka yi da kuɗaɗen.
“Akwai buƙatar a san abin da ake tarawa daga maƙudan kuɗaɗen da gwamnati ke samu bayan cire tallafin fetur. Kuma ya zama tilas a yi gyara, ta yadda za a riƙa bayyana abin da ake yi ko aka yi da kuɗaɗen. Saboda har yanzu babu wani takamaiman bayani. To dole a gyara wannan tsari.” Inji NEC.
A wurin taron wanda aka yi a ranar Laraba, an bayyana cewa an bai wa jihohi Naira biliyan 5 kowace, domin ta bayar da tallafi ga marasa galihu, ganin irin halin raɗaɗin tsadar rayuwar da ake ciki, tun bayan cire tallafin fetur.
Sai dai kuma NEC ba ta faɗi dalilin da ya sa ta yi wa jihohin kuɗin-goro ba, bisa la’akari da cewa al’ummar wata jihar ba su wuce miliyan uku ba, wata kuwa yawan jama’ar ta sun haura miliyan 10 ko ƙasa da haka.
Haka kuma NEC ta nuna damuwar ta ganin cewa Asusun Ajiyar Najeriya ya tsiyaye, daga Dala Biliyan 37.1 zuwa Biliyan 33.9 cikin wata bakwai.
Majalisar Tattalin Arzikin Najeriya ta bayyana damuwar ta ganin cewa Asusun Ajiyar Kuɗaɗen Najeriya a Waje, wato ‘External Reserves’, ya ragu sosai daga Janairu zuwa Julin 2023.
Duk da dai Majalisar ba ta bayyana abin da Najeriya ta yi da kuɗaɗen ba, ta fayyace cewa rumbun ajiyar ya ragu da kashi 8.3 bisa 100.
NEC ta ce a watan Janairu, 2023 akwai Dala biliyan 37.1 a cikin asusun. Amma a ƙarshen Yuli, kuɗin sun koma Dala biliyan 33.9.
Wata matsalar da Majalisar Tattalin Arziki ta ce ke fuskantar Asusun Ajiyar ita ce yadda buƙatar shigo da kaya ke ƙara yawa zuwa cikin Najeriya, amma kuma Najeriya ba ta fitar da wani abin a zo a gani in banda ɗanyen mai.
Matsalar faɗuwar darajar Naira a cikin gida a cewar NEC, abu ne da ke ƙara yin mummunan tasiri ga tattalin arzikin Najeriya.
Majalisar ta kuma koka dangane da yadda farashin kayan abinci ke ci gaba da cillawa sama ya na yin tashin-gwauron-zabo, a daidai lokacin da rashin aikin yi ke ƙara zama barazana ga matasan Najeriya.
Yawancin matsalolin dai sun faru ne sanadiyyar rashi ko ƙarancin masu zuba jari a Najeriya, sai kuma cire tallafin fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi tun a ranar 29 Ga Mayu.
Discussion about this post