Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana wa Kwamitin Malaman Addinin Musulunci masu shiga tsakanin ECOWAS da Sojojin Mulkin Nijar cewa shi ne da kan sa ke ta ƙoƙarin taka wa ECOWAS da wasu ɓangarori burki, don kada su afka wa Nijar da yaƙin ƙwatar dimokraɗiyya a ƙasar.
Tinubu wanda kuma shi ne Shugaban ECOWAS, ya bayyana haka lokacin da ya ke ganawa da malamai masu karakainar shiga tsakani da sojojin mulkin Nijar, domin a kauce wa yin amfani da sojoji a ƙasar.
Tinubu bai bayyana sunayen sauran ‘yan-gaje-ganin da ya ce su ma su na goyon bayan afka wa Nijar da yaƙi ba.
Amma dai ita ma AU na goyon bayan matakan sojan da ECOWAS ta yi barazanar ɗauka kan Nijar.
Sannan kuma har yanzu Faransa ba ta kwashe sojojin ta daga cikin Nijar ba. Kuma ba ta goyon bayan hamɓaras da gwamnatin Mohammed Bazoum da sojojin ƙasar su ka yi.
“Ina ta haƙilon taka burki domin kada a yi gaggawar afka wa Nijar da yaƙi. Baya ga ƙoƙarin dakatar da ECOWAS da na ke ta yi a kullum, akwai ‘yan-gaje-ganin da na a ƙarƙashin iko na su ke ba. To duk ni kaɗai ke taka burki kan afka wa Nijar.”
“Ina sanar da ku kai ko a safiyar nan, an yi ta kira na cewa me mu ke jira ne, a afka Nijar kawai, a-yi-ta-ta-ƙare. Amma na ce su jira tukunna, sai na yi magana da malaman da ta ƙoƙarin shiga tsakani. Don haka ku gaggauta yin mai yiwuwa.”
Haka Tinubu ya bayyana wa malaman, kamar yadda takardar da ke ɗauke da jawabin sa ta ƙunsa, wadda Kakakin Yaɗa Labaran Tinubu ɗin, Ajuri Ngelale ya aiko wa PREMIUM TIMES.
Sai dai kuma Tinubu ya shaida wa malaman cewa ba fa zai iya dakatar da afka wa Nijar da ƙarfin soja ba har wani tsawon lokaci. Don haka su hanzarta cimma matsaya abin karɓa a shiga tsakanin da su ke yi da Sojojin Mulkin Nijar.
Idan ba a manta ba, ECOWAS ta jaddada shirin kai wa Nijar hari, duk kuwa da roƙon da Tinubu ya yi na jingine batun, a taron shugabannin ECOWAS na baya a Abuja.
Cikin makon jiya ne dai Sojojin Mulkin Nijar su ka yi sanarwa ta bakin Shugaban Ƙasa Abdourahmane Tchiani cewa za ta bada mulki ga farar hula nan da shekaru uku. Amma ECOWAS ta ƙi amincewa, bisa dalilin cewa shekaru uku sun yi nisa.
Discussion about this post