Majalisar Dattawan Najeriya ta cimma rattaba rashin amincewa Shugaba Bola Tinubu ya tura sojojin Najeriya, domin su afka wa Jamhuriyar Nijar da yaƙi, domin ƙwato mulki daga hannun sojoji.
Maimakon haka, majalisar ta shawarci Tinubu da ECOWAS ƙungiyar da ya ke jagoranta, cewa su nemi duk wata hanyar da za a sasanta matsalar Nijar ta hanyoyin siyasa da diflomasiyya.
Dama kuma wannan jaridar ta buga labarin cewa Sanatocin Najeriya sun ce ba su yarda a kwashi sojojin Najeriya su tafi yaƙi Jamhuriyar Nijar ba.
A ranar Juma’a ce dai Shugaba Tinubu ya aika wa Majalisar Dattawa wasiƙar sanar da su shirin sa na afka wa Nijar da yaƙi, idan wa’adin kwanaki bakwai su ka cika sojojin Nijar ba su damƙa mulki a hannun hamɓararren shugaban ƙasa, Mohammed Bazoum ba.
A matsayar da Majalisar Dattawa ta cimma a ranar Asabar, sun amince da wasu matakan da ECOWAS da Najeriya su ka ɗauka, amma ba su amince da yin amfani da ƙarfin soja ba.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanto matsayar da su ka cimma.
Ya ce Majalisa ta na nusar da Tinubu cewa bai nemi amincewar ta ba kafin ya yanke tunanin yin amfani da sojojin Najeriya su kai yaƙi Nijar, a ƙarƙashin ECOWAS.
“Majalisar Dattawa ta jinjina wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a matsayin sa na Shugaban ECOWAS, shi da sauran shugabannin ƙasashen da ke cikin ƙungiyar, dangane da ƙoƙarin da su ke yi na neman maida dimokraɗiyya a gwamnatin Nijar.
“Sai dai kuma su na jan hankali cewa Shugaba Tinubu ya ci gaba da tuntuɓar sauran shugabanni na ƙasashen ECOWAS, domin su shawo kan matsalar shugabanci a Nijar ta hanyoyin siyasa da diflomasiyya, amma ba tare da an yaƙi ba.
“Kuma Majalisar Dattawa ta yi tir da juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar, sannan ta na fatan a shawo kan matsalar cikin lalama.”
Har yanzu dai hamɓararren Shugaban Nijar, Bazoum ya na tsare a hannun sojojin juyin mulkin Nijar.
Discussion about this post