Hukumar Kula da Ƙananan Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), ta ce an sallami ƙananan yara 4204 waɗanda Boko Haram su yi wa horon ta’addanci.
An sallame su daga kurkukun sojoji ranar Laraba, a Maiduguri, babban birnin jihar Barno.
Ƙananan yaran waɗanda ke tsare a hannun sojoji, an sallame su tare da damƙa su ga gwamnatocin jihohin Barno, Yobe da Adamawa domin maida su su ci gaba da rayuwa cikin jama’a.
Hukumar UNICEF ce ta damƙa su a bisa jagorancin Manajan Kare Rayukan Ƙananan Yara na UNICEF da ke Maiduguri, Samuel Sesay.
“Wannan tsarin damƙa ƙananan yara dai yarjejeniya ce da aka sa wa hannu tsakanin Gwamnatin Tarayya da Majalisar Ɗinkin Duniya, domin tabbatar da cewa an fitar da ƙananan yaran da ke da alaƙa da masu hare-haren makamai an cire su daga wuraren da sojoji ke tsare da su.
An ƙulla wannan yarjejeniya ce a cikin 2022.
“An yi yarjejeniyar ce domin tabbatar da cewa yaran da suka gudo daga hannun Boko Haram ko kuma waɗanda Boko Haram su ka sako, ba su daɗe tsare ba a hannun sojoji.
“Yarjejeniyar ta ƙunshi adadin wane lokaci yaran za su zauna tsare a hannun sojoji, wane lokaci za a sake su, ta yaya za a sake su, sannan kuma idan an sake su, ya za a yi da su.” Haka Sasey ya yi ƙarin bayani.
An damƙa yaran ga jami’an Ma’aikatar Harkokin Mata daga jihohin uku na Barno, Yobe da Adamawa.
“Za a tabbatar an kare rayukan dukkan ƙananan yaran da ke da alaƙa da Boko Haram ga Ma’aikatar Harkokin Mata, kuma za a ba su tallafin da yarjejeniya ta ce a ba su.”
Haka Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Barno, Zuwaira Gambo ta bayyana.
Zuwaira dai ta samu wakilci ne daga Babban Sakataren Riƙo na Ma’aikatar Harkokin Mata ta Jihar Barno z Mohammed Hamza
Discussion about this post