An tsince gawar wata budurwa mai shekaru 18 mai suna Wassa Joel wanda yan fashi suka kama ta a daji suka yi lalata da ita har sai da ta yi sallama da duniya.
Wannan abin tashin hankalin ya auku ne ranar Asabar din da ta gabata bayan yarinyar ta bar gida da yamma zuwa wwani kauye da goggonta take mai suna Lakanviri dake da nisan kilomita 10 daga garin Jalingo.
An tsinci gawar marigayiya Wassa a kusa da wani tsauni a Jalingo.
Yayan mamaciyar Ayuba Solomon ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ana jimamin wannan rashi a gidan su.
“ A ranar Asabar da yamma Wassa ta bar gida dake kusa da gidan Bishop za ta Lakanviri. A hanyar ta ne ta ci karo da wasu ‘yan fashi da dauke da bindigogi. A nan ne fa suka kamata da karfin tsiya suka yi lalata da ita har sai da sheka lahira.
“Wani yaro ne ya gano gawar ta a hanyarsa na debo itace da yake siyarwa. Daga nan sai ya sanar da iyayen ta da sauran mutane .
Ko da aka dauki gawar aka kai asibiti, sai likita ya tabbatar cewa fyade aka yi mata na rashin Imani da hakan ya kai ga ta rasa ranta.
Discussion about this post