Rundunar Sojojin ta 82 da ke Enugu ta gargaɗi sojojin da aka tura kula da shingayen tsaron kan titina cewa su guji karɓar kuɗaɗe daga hannun direbobi, kuma su daina aikata duk wani abin da zai zubar da darajar aikin soja.
An yi masu wanna gargaɗin ne a lokacin da ake masu wata lacca dangane haƙƙoƙin sojojin da aka tura kula da ababen hawa a shingayen kan titina.
Cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojojin Najeriya ta 82 da ke Enugu ya fitar, Jonah Unuakhalu ya ce an shirya laccar tare da gudanar da ita a Barikin Sojoji na Abakpa da ke Enugu.
“Sojojin Najeriya su na ayyukan tsaro a kan titinan ƙasar nan, saboda matsalar tsaron da ake fuskanta, wanda ya zama babbar barazana ga zamantakewar ƙasar nan.
“Duk da muhimmancin shingayen titinan da sojoji suka kafa a wurare daban-daban, ana samun ƙorafe-ƙorafe daga jama’a da dama na wasu ɗabi’un da wasu sojoji ke nunawa ko aikatawa, waɗanda ba su dace ba a shingayen tsaro da binciken motoci.
Abubuwan da su ke aikatawa kuma ake kuka da su kuwa, su na rage martaba da darajar aikin soja, da kuma kawo cikas ga dalilan kafa shingayen ɗungurugum.” Inji Laftanar Kanar Unuakhalu.
Ya ci gaba da cewa, “Su shingayen binciken motoci a kan titina matakan tsaro ne da hukuma ta ƙirƙiro domin sa-ido kan zirga-zirgar motoci da jama’a a yankin da aka kafa shingen.
“Wani muhimmancin shingayen sun haɗa tabbatar da bin doka da oda, tsaro da kuka hana cinkoson motoci kan titi.”
Ya ƙara da cewa a wurin taron an kuma gargaɗi sojojin a kan irin horo da hukuncin da doka ta tanadar ga duk wanda aka kama ya na karɓar kuɗi wurin direbobi.
Discussion about this post