Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta ci moriyar fasahar zamani sosai, domin faɗaɗa hanyoyin ci gaban tattalin arzikin Najeriya, wanda hakan ya zama tilas domin inganta rayuwar al’umma.
Tinubu ya bayyana haka a ranar Laraba, yayin da wakilan mashahuriyar manhajar duniya, wato Google (West Africa) suka kai masa ziyara.
Sun kai ziyarar ce a bisa jagorancin Darakta Olumide Balogun, inda Tinubu ya shaida masu cewa gwamnatin sa ta himmatu wajen yin amfani da ilmi da fasaha, domin inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
“Mun shiga shugabanci ne domin mu inganta rayuwar al’umma, tare da yin la’akari da cewa ilmi shi ne gishirin da ke ƙara wa ingancin rayuwar ‘yan Najeriya nagarta
Tinubu ya ce sun zo ne domin su wanke wa matasa tukunyar da su tuƙa tuwon gobe, domin sai an wanke tukunyar sannan tuwon zai yi zaƙi.
Sannan ya shaida wa tawagar cewa matasan Najeriya su ne kashi 65 bisa 100 na masu hanƙoron ɗabbaƙa ajandar ci gaba a Najeriya.
“Mun ɗauki ilmi da matuƙar muhimmanci, domin shi ne babban makamin yaƙi da talauci.
“Bunƙasa tattalin arziki ta hanyar fasahar zamani da sadarwa sun su ne mahangar da mu ke ƙoƙarin mu ga mun inganta.
“Haɗa kai da Google domin mun bunƙasa tattalin arzikin mu shi ne abin da mu ke muradi.
“Saboda matasan mu na da ƙwarewa, gogewa, basira kuma matasan ƙwarai ne.” Inji Shugaba Tinubu.
Sannan ya yi kira ga Google ya haɗa hannu da Najeriya da Najeriya domin atantance tsare-tsaren hada-hada a ƙasar nan, ya na mai cewa al’mumma mai mutane sama da miliyan 200 fa ba abin wasa ba ce.
Shugaban na Google na Afrika ta Yamma, ya ce sun zo Najeriya domin su tabbatar da cewa a shirye su ke su haɗa hannu domin kamfanin ya samar da ci gaban fasahar zamani a Najeriya.
Discussion about this post