An tsinci gawar wata mai wa’azi a ɗakin otal ɗin da wani Babban Limamin Coci ya kai ta cikin dare.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Abiya sun bayyana damƙe Babban Lamamin Cocin Pentacostal, dangane da mutuwar wata mata mai wa’azi, wadda ta mutu a ɗakin otal ɗin da shi da ita su ka shiga cikin dare.
Lamarin ya faru cikin Ƙaramar Hukumar Obingwa, inda tuni aka kama Bishop Timothy Otu, Babban Limamin Cocin Agape Evangelical Ministry.
An tabbatar da cewa Babban Limamin ne ya kai ta matar mai suna Happiness Exhieze, ɗakin otal ɗin.
Kafin rasuwar ta, Happiness ta na da shekaru 43, kuma ta na da ‘ya’ya uku.
Ta rasu a cikin ɗakin otal ɗin da Otu ya kai ta, kamar yadda ‘yan sanda su ka bada sanarwa.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Abiya, Maureen Chinaka, ta tabbatar da haka a cikin wata sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis. Ta ce sunan otal ɗin da aka tsinci gawar Jubilee Guest House.
Kafin rasuwar ta, mai wa’azin dai ta na da miji, wanda ke can ya na zaune a Bayelsa.
Chinaka ta sanar wa manema labarai cewa Bishop Otu ya shiga ɗakin otal ɗin tare da marigayiyar, wajen ƙarfe 9:25 na dare, a ranar 12 Ga Agusta.
Ta ce wani ma’aikacin otal ɗin ne mai suna Godwin Akpan ya kai rahoton mutuwar matar ga ofishin ‘yan sanda da ke Isiala-Ngwa.
Ya shaida masu cewa ya shiga ɗakin wajen 12 na dare a ranar da matar da Otu suka kama ɗakin kuma suka shiga.
Akpan ya shaida wa ‘yan sanda cewa yayin da ya shiga ɗakin wajen 12 na dare.
“Ya same ta a mace kuma babu tufafi a jikin ta, ga wata kumfa fara ta na fita ta baki da hancin ta. Amma kuma shi Babban Limamin Cocin da ya kai ta ɗakin otal ɗin, ya rigaya ya fice, baya nan.”
Ta ce an maida batun zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Hedikwatar ‘Yan Sandan Jihar Abiya, domin bincike.
“Ita kuma gawar an ajiye ta a ɗakin adana gawarwaki, kafin a gudanar da binciken musabbabin mutuwar ta.”
Discussion about this post