Sheikh Ibrahim Ɗahiru Bauchi, wanda ya wakilci Sheikh Ɗahiru Bauchi yayin da manyan malaman Najeriya su ka je Nijar, a matsayin jakadun shiga tsakanin sojojin mulkin Nijar da ECOWAS, ya bayyana cikakken bayanin da Janar Abdourahmane Tchiani ya yi masu dangane da halin da hamɓararren shugaban ƙasar Nijar, Mohammed Bazoum ke ciki.
Yadda Aka Yi Wa Bazoum Juyin Mulki:
“Janar Abdourahmane Tchiani ya shaida mana cewa tun da farko sun tsara cewa ba za su taɓa yarda a kashe ko mutum ɗaya ba yayin juyin mulkin. Ya ce kuma ba a kashe kowa ɗin ba.
“Ya ce mana wasu abubuwa ne su ka ga sun tunkaro Nijar da Najeriya, shi ya sa su ka yi sauri su ka ƙwace mulki, domin hana afkuwar lamarin.
“To kuma ya shaida mana cewa idan komai ya daidaita za su bada mulki ga farar hula.”
“Bazoum Lafiya Ƙalau Ya Ke Ko Wayar Hannun Sa Ba A Karɓe Ba”:
“Lokacin da mu ka bar Najeriya mun tafi da nufin yin magana kan Bazoum, domin yiwuwar ganawa da shi.
“Amma a bayanan da mu ka yi da Shugaban Sojojin Mulkin, sai muka fahimci ba za mu yi maganar ganin Bazoum ba.
“Amma tun tambayi cewa ana cewa Bazoum ba shi da lafiya, sai Janar Tchiani ya shaida mana cewa lafiya ƙalau ya ke. Akwai likitan sa da su ke tare shekaru da dama, har yanzu shi ke kula da lafiyar sa.
“Tchiani ya shaida mana cewa ko wayar Bazoum ba a ƙwace ba. Kuma a kullum ya na yin waya da duk wanda ya ga dama. Sai dai kuma Janar Tchiani ya ce duk wanda Bazoum ya yi waya da shi, su na jin duk abin da su ke tattaunawa.”
‘Iyalan Bazoum Duk Mun Ce Su Tafi Ƙasar Waje, Shi Da Ɗan Sa Ɗaya Kaɗai Ke Tsare’:
Janar Tchiani ya shaida mana cewa lokacin da suka yi juyin mulki, sun ga yanayin da ƙasar ke ciki, sai suka ce iyalan Bazoum su tafi ƙasar waje, domin idan su ka zauna a Nijar, to ba su da garantin iya tsare lafiyar su.
“Janar Tchiani ya shaida mana cewa su ma da suka yi juyin mulkin ƙoƙarin iya tsare kan su suke yi, ballantana tsaron iyalan Bazoum idan su na gida.”
‘Dalilin Hana Tawagar Abdulsalami Ta ECOWAS Shiga Yamai’:
Janar Tchiani ya shaida mana cewa a madadin Gwamnatin Nijar, ya na bada haƙurin rashin ganawar da ya yi da tawagar da ECOWAS ta tura, saboda waɗansu dalilai.”
A hirar sa da Sashen Hausa na VOA, Ibrihim Ɗahiru Bauchi ya ce, “Janar Tchiani ya shaida masu cewa an hana tawagar shiga Yamai, saboda a lokacin rayukan jama’a a ɓace ya ke, saboda haushin an ƙaƙaba wa Nijar takunkumi, har an yanke wuta, alhali kuwa hatta asibitoci da wutar su ke amfani.”
“Tchiani ya shaida mana cewa a lokacin mahukuntan Nijar na tsoron kada wani abu ya same su, idan suka shigo cikin gari har mutane su ka ga tawagar ECOWAS ce.
“Ya ce dalili kenan aka tsayar da su aka tattauna a filin jirgin saman Yamai, su ka koma Najeriya.”
Discussion about this post