Rundunar ƴan sandan jihar Delta ta kama wasu maza 67 da ake zargi ƴan luwadi ne a kauyen Ekpan dake karamar hukumar Uvwie.
Kakakin rundunar Wale Abass ya sanar da haka wa manema labarai a ofishin ‘yan sanda dake Ekpan ranar Talata.
Abass ya ce dakarun ‘yan sandan sun kama wadannan mutane ranar Lahadi yayin da suke sintiri a Uvwie.
Ya ce jami’an tsaron sun kama wadannan mutane ne yayin da suke taron daurin aure a wani otel dake hanyar Refinery a Uvwie.
“A ranar 27 ga Agusta da misalin karfe tara na dare ‘yan sandan dake aiki a Ekpan sun kama wani namiji sanye da kayan mace.
“Da farko mutumin ya fada wa jami’an tsaron cewa shi dan wasan kwaikwayo ne amma daga baya sai ya fada musu ce yana hanya ne za shi daurin auren abokan sa ‘yan luwadi irinsa a wani otel.
“Jin haka ya sa jami’an tsaron suka tasa keyar mutumin zuwa wurin daurin auren inda suka iske dandazon maza sanye da kayan mata ana daurin aure.
“Da dama daga cikin su sun gudu amma jami’an tsaron sun kama mutum 67 a wurin bukin.
“Dakarun sun kama rigunan mata da mazan ke amfani da su domin taron daurin auren, kwalban kodin guda daya, kofuna uku da kwayar Canadian Loud a ciki, fakitin ganyen SK, fakitin kwayar Tramadol daya da kwayar Molly guda hudu.
Abass ya ce Kamen da suka Yi zai zama darasi ga duk wanda ke da niyar karya dokar hana madigo da luwadi da gwamnati ta Saka.
Daya daga cikin mutanen da aka kama Daniel Pius ya bayyana wa jami’an tsaron cewa shi ba dan luwadi bane amma ya zo wajen taron ne domin neman abinci.
“Ni tela ne kuma nakan yi wa mutane kwaliya lokacin buki abin da ya kawo ni wurin nan kenan amma ni ba dan luwadi bane.
Discussion about this post