Rundunar Ƴan sandan jihar Legas ta kama wata mata tela, mai suna Nsikat Etim mai shekaru 26 bisa laifin lakadawa dan uwan mijinta da matarsa dukan tsiya.
‘Yan sanda sun kai karar Nsikat dake zama a lamba 411 layin Dopemu dake Agege, bisa laifukan da suka hada da tada husuma, cin zarafi, da wuce gona da iri.
Dan sandan da ya shigar da karar Hyacinth Agada ya ce Nsikat ta aikata haka ranar 3 ga Agusta a lamba 6 layin Ijaiye dake Papa Ashafa a Agege.
Agada ya ce a wannan rana Nsikat tare da wani mutum da ‘yan sanda ke neman sa ruwa a jallo sun je gidan sirikinta inda a nan suka taru suka yi wa dan uwan mijinta Iniabasi Umor da matarsa dukan tsiya.
Ya ce Nsikat ta ciji matar sirikinta a kunnen.
A kotun Nsikat ta musanta laifukan da ake zarginta da su.
Alkalin kotun O. O. Adeosun ta bada belin Nsikat akan naira 50,000 tare da gabatar da shaidu biyu a kotu
Adeosun ta ce za a ci gaba da shari’a ranar 31 ga Agusta.
Discussion about this post