Rundunar ƴan sandan Kaduna tare da hadin gwiwar na Katsina sun cafke wani dan damfara da ya siyar wa matasa takardan daukan aiki na boge na Kamfanin wutar lantarki na Kaduna.
‘Yan sandan sun kama Abdulrahman Junaidu a Funtuwa jihar Katsina bayan ya siyar wa Abdullahi Abubakar da Isiya Iliyasu takardun daukan aiki na boge.
Dubun Junaidu ya cika ne a ranar da Abubakar da Iliyasu suka gabatar da takardun daukan su aiki a matsayin ma’aikatan kamfanin wutat lantarki dake Zaria, jihar Kaduna.
Sakamakon binciken da jami’an tsaron suka yi ya nuna cewa Junaidu na aiki da wani basakwace Aliyu Sani da tare suke damfarar mutane kudade suna basu takardun daukan aiki na boge.
Kakakin Kamfanin wutar lantarki na Kaduna ya tabbatar cewa rundunar ‘yan sanda sun fara farautar Sani domin hukunta shi bisa laifin da ya aika ta.
“Ina tabbatar da cewa da zarar jami’an tsaron sun kammala gudanar da bincike za a kai Junaidu da Sani kotu domin yanke musu hukunci.
Ya yi kira ga mutane da su rika taka tsantsan da irin su Junaidu, ƴan damfara masu damfarar mutane da sunananbza su sama musu aiki, sannan daga karshe kuma abin ya zama ba haka ba.
Discussion about this post