Ƴan bindigan da suka Yi garkuwa da ɗalibai masu bautan kasa su 8 a jihar Zamfara sun bukaci a biya kudin fansan naira miliyan 4 kan daya daga cikin su.
Mahaifin Emmanuel Ettah ɗaya daga cikin ɗaliban da aka yi garkuwa da su mai suna Glory Thomas ya bayyana haka da yake hira da Talbijin ɗin ‘Channels’ ranar Juma’a.
“Sun kira ni ta waya suka ce in biya Naira miliyan hudu kafin su saki ‘ya ta. Na Yi magana da ‘ya ta sannan na tambaye su yadda zan biya kudin. Sai suka ce in nemi Kamfanin sufuri na AKTC.
“Tun daga lokacin ba su kara kira na ba sannan ban sake ji daga wurin su ba da kuma ‘ya ta.
Zuwa yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ba su ce komai ba kan garkuwan da aka yi da daliban.
Wata majiya mai tushe a rundunar sojin Najeriya ya tabbatar cewa dakarun sojin Najeriya na gudanar da aiki a dazukan jihar domin kamo maharan da ceto ɗaliban.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin ƴan bindiga sun tare hanya sun yin kwashe ‘yan bautan kasa 8 yayin da suke hanyar su ta zuwa aikin bautan kasa a jihar Sokoto daga Akwa-Ibom.
Duk wadanda aka yi garkuwa da su na cikin wata mai kiran bus ta Kamfanin sufuri motocin Akwa-Ibom AKTC daga Uyo kan zuwa Sokoto.
Daga cikin waɗanda aka yi garkuwar da su akwai Emmanuel Esudue, kuma dukkan su wayoyin su a kashe.
Sannan kuma akwai wata mai suna Betty Udofia.
Sai dai kuma wani mai suna Edidiong Richard, ya rubuta a shafin sa na Facebook cewa ‘yan bindigar sun tuntuɓi iyayen Udofia, inda har su ka nemi sai an biya su fansar Naira miliyan 4 tukunna kafin su sake shi.
Discussion about this post