Ƙasashen da ke ƙarƙashin Ƙungiyar Ƙawance ta BRICS su biyar, sun amince su yi wa ƙasashen Ajantina, Masar, Saudi Arabiya, Iran, UAE da Habasha rajista, domin ƙarin ƙwari da ƙarfin ƙungiyar.
BRICS wadda ta ƙunshi Brazil, Rasha, Indiya, Chana da Afrika ta Kudu, sun amince da yi wa ƙasashen shida rajista, ta bakin Shugaban Afirka ta Kudu, Ceril Ramaposa, kamar yadda ya sanar a shafin soshiyal midiya na X, wato Tiwita.
“BRICS ta maida hankali wajen kafa sabon babi a duniya, wanda ke cike da adalci, gaskiya, kuma mai yalwa a doron duniya.” Inji Ramaposa.
Shugaban na Afrika ta Kudu ya yi wannan bayani a cikin jawabin sa wurin taron BRICS, wanda a yanzu haka ke gudana a Johannesburg, Babban Birnin Afrika ta Kudu.
Ramaposa ya ce za a shigar da sabbin mambobin shida cikin ƙungiya a ranar 1 Ga Janairu, 2024.
Ya ci gaba da cewa ƙasashe 23 ne su ka cika fam ɗin neman shiga BRICS, cikin su har da guda shida ɗin da aka amince a yi masu rajista a yanzu.
Sauran manyan ƙasashen sun haɗa da Najeriya da Ghana, kamar yadda CNBC ya ruwaito.
Ramaposa da Shugaban Brazil, Luiz Silva sun ce sun bar ƙofa a buɗe domin yiwuwar ƙara yi wa wasu ƙasashe rajista nan gaba.
Silva ya ce tsarin curewar hada-hadar duniya wuri ɗaya bai yi nasara ba, don haka lokaci ya yi da ƙasashe masu tasowa za su zaburas da kan su da kan su, “ganin akwai barazanar afkawa yaƙin makamin ƙare-dangi.” Haka dai Reuters ta ruwaito.
Shi kuwa Shugaban Chana Xi Jumping, ya faɗa a ranar Alhamis ɗin yau cewa faɗaɗa ƙofar shigowar wasu ƙasashe a cikin BRICS, “alama ce mai nuna fara kafa ƙungiyar a cikin haɗin kai.”
Shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), Mohammed bin Zayed, wanda ƙasar sa mamba ce a cikin Bankin NDB, ya ce ya yi matuƙar murna ganin an shigar da ƙasar sa a cikin Ƙungiyar BRICS.
Sauran waɗanda suka yi jawabai har da Shugaban Brazil, Lula da Silva, wanda ke a sahun gaban ganin Kungiyar BRICS ta fitar da kuɗaɗen ta wanda za ta riƙa hada-hada da su a tsakanin ƙasashen da ke cikin ƙungiyar.
Discussion about this post