Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta yi aiki tuƙuru domin ta bi dukkan hanyoyin da suka dace ta janyo hankalin masu zuba a Najeriya.
Tinubu ya bayyana haka a ranar Laraba, inda ya tabbatar wa masu sha’awar zuba jari cewa tsare-tsaren gwamnatin sa domin daidaita tattalin arziki zai samu ƙarin tagomashi, yayin da aka maida hankali sosai wajen kawar da duk wasu matsaloli, ƙalubale da barazanar da ke haifar wa masu zuba jari cikas wajen yin harkokin kasuwancin su a Najeriya.
Ya ana bada fifiko wajen inganta ayyuka, sake nazarin biyan haraji da kuma inganta matakan tsaro.
Ya yi wannan bayani a lokacin da ya ke karɓar baƙuncin Babban Daraktan Inganta Makamashi, Albarkatun Ƙasa da Gas na Turai, Afrika da Gabas ta Tsakiya a Bankin Standard Chartered, Ade Adeola.
Ya ce gwamnatin sa ta fara aiki sosai wajen kawo gagarimin sauyi a cikin sauƙi domin sauƙaƙa wa dukkan maso son zuba jari gudanar da kasuwancin su.
“Mun maida himma sosai wajen ƙarfafa haɗin-guiwa, inyantawa da bijiro da hanyoyin sauƙaƙa wa masu son zuba jari gudanar da hada-hadar su.
Shugaba Tinubu ya shaida wa tawagar cewa a yanzu haka ana nan ana ci gaba da yi wa tsarin haraji garambawul a Najeriya, ta hanyar yin la’akari da tsarin sauran ƙasashen da suka ci gaba a duniya, domin samun bunƙasar yalwar tattalin arziki a Najeriya.
Da yake jawabi, Adeola ya ce Bankin Standard Chartered Bank a shirye ya ke ya zuba jari a Najeriya, musamman a fannin inganta makamashi da gas.
Discussion about this post