A ƙoƙarin da ake yi domin a tserar da darajar Naira, kamfanin NNPCL zai ciwo bashin Dala Biliyan 3 daga bankin Afrexim Bank a cikin gaggawa.
Wata sanarwar da ta fito daga NNPC, wadda aka sa wa hannu a ranar Laraba, ta ce an rattaba hannun yarjejeniyar amincewa da bashin a Hedikwatar Afrexim Bank da ke Cairo, babban birnin Misra.
Za a riƙa kamfatar ɗanyen man Najeriya ana sayarwa ana biyan bashin da kuɗin.
NNPCL ta ce ta ciwo bashin ne domin ta tallafa wa ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi wajen neman yadda za a yi Dala ta wadata a ƙasar nan, ta yadda farashin ta zai faɗi ƙasa, ita kuma Naira darajar ta ta ƙara ɗagawa sama sosai.
Naira ta ƙara shiga matsanancin garari tun bayan da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sake ta a kasuwa domin ta yi kiwo, ba tare da makiyayin ta ba.
Cikin makon da ya gabata kuma sai da ta kai a kasuwar ‘yan canji an sayar da Dala ɗaya har Naira 960.
Ɗan jarida, mai sharhin al’amurran yau da kullum, Aliyu Ɗahiru Aliyu, ya bayyana ra’ayin sa dangane da wannan bashin kuɗin lukudin da NNPCL zai ciwo, inda ya ce:
“Bashin da NNPC ta ciyo shi zai sa Dala ta yawaita a Najeriya. Wannan shi zai sanya farashin ta ya sauko saboda akwai ta a ƙasa. Bashin kuma za a biya shi ne da man fetur ba da kuɗi ba. Sai dai wani zai yi tambayar ko me zai faru idan a gaba samun Dala ɗin mu ya ragu tun da mu dama da fetur muka fi samun Dala, kuma ga shi za a bayar da fetur ɗin a biyan bashi?
“Amsar ta dogara ne ga sababbin matatun man fetur ɗin da su Dangote za su buɗe. Idan suka buɗe, za su shigo da DalaNajeriya kuma hakan zai ƙara wa Naira ƙarfi. Amma idan ba su buɗe ba, kuma muka ci gaba da zaman siyo kayan ƙasashen waje maimakon mu mu fitar, to za a iya komawa gidan jiya, wato Naira ta ƙara faɗuwa ƙasa warwas.”
Zubewar Darajar Naira: Shawarwarin Masana:
Kwanan nan kuma wasu ƙwararrun masana suka bada shawarar yadda gwamnati za ta hana darajar Naira komawa daidai ta takardar tsire ko balangu.
Karin maganar da Bahaushe ke cewa, ‘idan ka ji ana sa-toka-sa-katsi, to baba ce ba ta ji a wurin rini ba’, ta yi daidai a halin da ake ciki yanzu da Naira ke ci gaba da fuskantar zubewar daraja a duk lokacin da ta yi goyayya da dala a kasuwannin canjin kuɗi.
Ganin halin da Dala ke ciki ne wasu ƙwararrun masana da ake kira ‘Agora Policy’ da ke Abuja, sun fito da rahoton shawarwarin da su ka ce idan aka yi amfani da su, to Naira za ta tsira da mutuncin ta, har darajar ta ta koma kamar da can baya.
Masanan sun ce idan CBN ya yi amfani da shawarwarin, to za a iya cimma burin da ake ƙoƙarin yi na hana Naira ci gaba da zabgewa.
A cikin wani sabon rahoton da ‘Agora Policy’ ya fitar a ranar Litinin, ya ce Najeriya na buƙatar a ƙara angizo Dala a cikin ƙasar nan, ta yadda tattalin arzikin ƙasar nan zai samu hada-hadar ruwan kuɗi masu yawan da za su sa Dala ta daina yin ƙaranci.
Dala dai ta ƙara yin daraja a Najeriya, tun bayan da ta yi tsada daga N780 a kasuwar ‘yan canji, zuwa har Naira 960 a makon jiya.
A kasuwar hada-hadar zuba jari kuwa, Dala ta tashi daga N465 a farashin gwamnati a cikin Mayu, 2023 zuwa N780, farashin da take a bankuna yanzu.
Masanan sun ce don gudun kada a kullum a riƙa tuma tsalle a wuri ɗaya, ya kamata duk wani tsare-tsarwen tattalin arziki a riƙa yin sa kafaɗa-da-kafaɗa da lamarin musayar kuɗaɗen waje da tsarin hada-hadar kuɗaɗe.
Discussion about this post